An Shiga Jimami Bayan Tsohon Minista a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Shiga Jimami Bayan Tsohon Minista a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Majalisar zartarwa ta yi alhinin rashin tsohon Ministan ilimi a Najeriya, Farfesa Fabian Osuji a yau Alhamis
  • Marigayjn ya rasu a jiya Laraba 28 ga watan Faburairu bayan ya dawo daga kasar Amurka a ranar Asabar
  • Fabian ya rike mukamin Ministan ilimi a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon Ministan ilimi a Najeriya, Farfesa Fabian Osuji ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya.

Marigayin, Osuji ya rasu ne a jiya Laraba 28 ga watan Faburairu ya na da shekaru 82 a duniya, cewar The Nation.

An yi babban rashi bayan rasuwar tsohon Minista a Najeriya
Marigayin ya rike mukamin Minista a mulkin Olusegun Obasanjo. Hoto: Prof. Fabian Osuji.
Asali: Facebook

Yaushe marigayin ya rike mukamin Minista?

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gamu da cikas a CBN, wanda ya naɗa ya yi watsi da muƙamin kan dalili 1

Wata majiya daga iyalinsa ta tabbatar cewa Osuji ya dawo daga Amurka a ranar Asabar inda ya yi jinya kan wata cuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fabian ya rike mukamin Ministan ilimi a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo.

An haifi marigayin a ranar 20 ga watan Janairun 1942 a jihar Imo inda ya halarci makarantar firamare da sakandare a jihar.

Daga bisani ya tafi Jami'ar Najeriya ta Nsukka a jihar Enugu da kuma Jami'ar Ibadan da ke jihar Oyo, The Source ta tattaro.

Farfesa ya taba aiki a Jami'ar St. John da ke birnin New York a Amurka daga shekarar 1997 zuwa 1999.

Martani Gwamnatin Tarayya kan rasuwar Farfesan

Majalisar zartarwa ta FEC ta yi alhinin mutuwar Farfesan wanda ya rasu a jiya Laraba e 28 ga watan Faburairu.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamnan APC ya tausaya, zai raba buhunan shinkafa da taliya ga talakawa a watan azumi

Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume wanda ya yi magana a madadin Majalisar ya bayyana rashin a matsayin mai wuyar cikewa.

Daraktan yada labaran Akume, Segun Imohiosen shi ya bayyana haka a yau Alhamis 29 ga watan Faburairu.

Akume ya ce tabbas an yi babban rashi na mutum mai ilimi wanda ya ba da gudunmawa sosai a bangarori da dama na kasar.

Jarumin fina-finan Nollywood ya rasu

Kun ji cewa fitaccen jarumin fina-finan a Najeriya ya rasu bayan fama da doguwar jinya a jihar Ogun.

Marigayin Jimi Solanke ya rasu ne bayan jeka-ka-dawo da aka ta yi da shi daga asibiti zuwa gida tun a watan Disambar 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel