Yan ta'adda
Wani lamari mai ban tausayi ya faru a garin Amagu Ihube a karamar hukumar Okigwe dake jihar Imo ranar Talata yayin da yan ta'adda suka kona dattijuwa da ranta.
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gano yadda 'yan Boko Haram suka tsara za asu kai hari kan jirgin kasan Abuja-Kaduna a cikin 'yan kwanakin nan masu zuwa.
Jama’a mazauna Onyagede da ke karamar hukumar Ohimini ta jihar Binuwai sun tsorata kan Kaiwa da kawowa wani helikwafta a yankin wanda ke sauke wasu irin sojoji.
An yi gagarumar arangama tsakanin mayakan Boko Haram da mayakan ISWAP a yankunan Kuwa Nguori da kauyen Ngoldiri dake kusa da Timbuktu da ke Damboa a Borno.
Wasu tsagerun 'yan bindiga sun farmaki lakcara a lokacin da yake shirin kai 'ya'yansa makaranta. An bayyana yadda lamarin ya auku a wani yankin Awka na jihar.
Wasu 'yan daba a yankin garin Muchala da ke kusa ta Mubi sun farmaki Lami Ahmadu Fintiri, matar Gwamna Ahmadu Fintiri. Sun raunata mutum daya cikin tawagarta.
A labarin da muke samu, wasu 'yan bindiga sun kashe mutum shida nan take tare da kwace kudaden da ke jikinsu a jihar Ondo, Lamarin ya kawo tashin hankali jihar.
An hallaka wani alkali yayin da yake yanke hukunci a jihar Imo, Kungiyar lauyoyin Najeriya sun ce hakan ba daidai bane, kuma za su dauki matakin da ya dace.
Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da farmakin da wasu miyagu suka kai kan caji ofis da ofishin INEC a jihar a safiyar Laraba wurin karfe 2:45.
Yan ta'adda
Samu kari