Borno: Zulum Ya Sanar da Abun Mamakin da Ya Faru da 'Yan Ta'adda Wanda Ba a Taba ba a Duniya

Borno: Zulum Ya Sanar da Abun Mamakin da Ya Faru da 'Yan Ta'adda Wanda Ba a Taba ba a Duniya

  • Farfesa Babagana Zulum na jihar Borno ya bayyana yadda 'yan ta'addan ISWAP da Boko Haram 90,000 suka tuba tare da mika wuya ga hukumomi
  • Ya sanar da cewa, hakan bai taba faruwa ba a tarihin ta'addanci a duniya cikin shekara daya rak a samu irin wannan nasarar ta yaki da miyagun
  • Gwamnan ya yabawa Buhari yadda ya kwato dukkan kananan hukumomin dake hannun 'yan Boko Haram 22 bayan ya hau mulki

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, yace sama da mambobin Boko Haram da ISWAP 90,000 ne suka mika ga hukuma cikin shekara daya.

Gwamnan yayin da yake jawabi a taron majalisar dinkin duniya karo na 77 da aka yi a New York, yace ‘yan ta’adda da kansu suka dinga mika wuya wurin sojoji, jaridar TheCable ta rahoto hakan.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari Kan Bayin Allah, Sun Kashe Rayuka

Zulum a UN
Borno: Zulum Ya Sanar da Abun Mamakin da Ya Faru da 'Yan Ta'adda Wanda Ba a Taba ba a Duniya. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Zulum yace wannan bai taba faruwa ba a ko ina a duniya kuma yanzu ta’addanci na zuwa karshe.

“Ina so in sanar da jama’a da suka tattaru a nan cewa a shekara daya da ta gabata, gwamnatin jihar Borno da gwamnatin tarayya ta karba sama da mutum 90,000 da suka tuba daga ta’addancin kungiyoyin Boko Haram da ISWAP.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Wannan bai taba faruwa ba a ko in a duniya. A tarihin duniya, ta’addanci na zuwa karshe. Na fara ganin haske a harkar. Zaman lafiya ga dukkan yankin arewa maso gabas, zaman lafiya ga dukkan Turai da zaman lafiya ga dukkan duniya.”

- Zulum yace

Gwamnan yayin yabawa shugaba Muhammadu Buhari, yace kananan hukumomi 22 daga cikin 27 na jihar ne ke hannun Boko Haram kafin Buhari ya hau shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

Dailin Da Yasa Na Yi Shiru Game da Rikicin Atiku da Gwamna Wike, Saraki Ya Magantu

Yace a yau babu karamar hukumar dake hannun ‘yan ta’addan a jihar.

“Gwamnatin jihar Borno tare da goyon bayan gwamnatin tarayya da kuma dukkan UN sun karfafa jajircewar al’ummomi.
“Sannan hakan ya tabbatar da gina zama lafiya da cigaba ga dukkan yankin arewa maso gabas na Najeriya.
“Alakar dake tsakanin zaman lafiya, tsaro da cigaba ya dace a sake assasa ta. Idan babu zaman lafiya, ba za a samu tsaro ba kuma idan babu tsaro, ba za a samu cigaba ba."

- Zulum yace.

Bidiyo: Mai Garkuwa da Mutane dake Watsin Daloli a Soshiyal Midiya Yana Zubda Hawaye a Hannun 'Yan Sanda

A wani labari na daban, bidiyon John Lyon, wanda ake zargi da kasancewa shugaban wata kungiyar garkuwa da mutane, ya bayyana yana zubda hawaye kamar karamin yaro yayin da ya shiga hannun 'yan sanda.

A wani bidiyo, wanda ake zargin da aka fi sani da Lion White, ya bayyana babu riga inda yake sanye da gajeren wando kadai a jikinsa.

Kara karanta wannan

Wike Ya Fallasa Ayu, Ya Bayyana Babban Mukamin da Yake So Idan Atiku Ya Ci Zabe

Asali: Legit.ng

Online view pixel