Sanata Ya Zargi Ali Modu Sheriff da Ƙoƙarin Jefa Ƙiyayya tsakanin Obi da Ƴan Arewa

Sanata Ya Zargi Ali Modu Sheriff da Ƙoƙarin Jefa Ƙiyayya tsakanin Obi da Ƴan Arewa

  • Sanatan Anambra, Victor Umeh ya zargi tsohon gwamnan Borno Ali Modu Sheriff da ƙoƙarin haifar da ƙiyayya ga Peter Obi a Arewa kafin zaben 2027
  • Ali Modu Sheriff ya yi iƙirarin cewa mutanen Arewa ba za su zaɓi Peter Obi ba a 2027 saboda yana da ra'ayin raba Najeriya kuma ya muzguna wa yan Arewa
  • Sanata Umeh ya kara da cewa Peter Obi na da haƙƙin yin kira ga shugaba Tinubu da ya yi murabus, yana mai cewa dimokraɗiyya ta ba shi wannan damar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Anambra - Sanata mai wakiltar Anambra ta Tsakiya, Victor Umeh, ya caccaki tsohon gwamnan jihar Borno Ali Modu Sheriff bayan kalamansa kan Peter Obi.

Sanata Umeh ya zargin tsohon gwamnan da yunƙurin jawo wa ɗan takarar shugabancin ƙasar karkashin jam'iyyar NDC, Peter Obi, bakin jini a yankin Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

2027: Martanin Kwankwaso ga Ali Modu Sheriff bayan ya ce su Obi ba za su kai labari ba

An yi martani ga Ali Modu Sheriff kan Peter Obi
Ali Modu Sheriff da dan takarar shugaban kasa a zaben 2027, Peter Obi Hoto: Ajid Saleh Ajid/Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Umeh ya dura a kan Peter Obi ne bayan hira da aka yi da shi a kafar Channels TV inda ya bayyana cewa Peter Obi ba zai samu kuri'a mutanen Arewa ba.

Umeh ya yi raddi ga Ali Modu

A ruwayar jaridar Punch, A ranar Talata, Umeh ya bayyana cewa tsohon gwamnan yana tunani da tsofaffin ra'ayoyin siyasa da suka wuce, kuma Najeriya ta ci gaba an wuce wurin rabuwar kai.

Umeh ya ce duk wanda ya tashi ya ce Arewa ba za ta zaɓi Peter Obi ba, yana ƙoƙarin tayar da yaƙi da ya ƙare shekaru 56 da suka wuce.

Umeh ya ce Ali Modu na son dawo da tsohuwar siyasa Najeriya
Peter Obi tare da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Twitter

Ya ƙara da cewa ba a sake koma wa ruwa ba, kuma yan Najeriya sun samu ci gaba da wayewar da ake bukata wajen cicciba kasa ta yi gaba.

Sanata Umeh ya bayyana Obi a matsayin ɗaya daga cikin fitattun mutane da Najeriya ta samar, wanda ya ke adawa muraran da tashin hankali.

Kara karanta wannan

Matar Tinubu za ta tara matan Kano ta ba su tallafin kayan sana'a

Umeh ya kare kalaman Obi

A ci gaba da martaninsa, Umeh ya bayyana cewa Peter Obi yana da dama da yancin siyasa na neman Shugaban kasa mai ci ya yi murabus.

Sanatan ya ce ko shi Tinubu da kansa ya yi irin wannan kira a zamanin gwamnatin Jonathan, don haka dimokraɗiyya ta ba Obi damar yin haka.

Ya kuma nuna damuwarsa game da matsin rayiwa da ake ciki, musamman tsadar man fetur da ke haifar da hauhawar farashin kayayyaki a duk faɗin ƙasar.

Obi ba zai samu Arewa ba - Ali Modu

A baya, kun samu labarin cewa tsohon gwamnan Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ce Peter Obi ba zai samu goyon bayan mafi yawan masu kada kuri'a daga Arewa ba a zaben 2027.

Ya bayyana cewa duk da an samu hadin kai a tsakanin Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wannan ba zai jawo hankalin Kanawa wajen zaben yan takarar ba saboda wasu dalilai.

Tsohon gwamna Ali Modu Sheriff ya kuma bayyana cewa a yanzu haka, mutanen Kano za su juya wa zaben Kwankwaso baya matukar yana a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng