Zakuna Sun Yi Kaca-Kaca da Wasu ’Yan Ta’adda da Sunan Jihadi a Mozambique

Zakuna Sun Yi Kaca-Kaca da Wasu ’Yan Ta’adda da Sunan Jihadi a Mozambique

  • Jami'an tsaro a kasar Mozambique sun bayyana yadda zakuna suka yi kalace da wasu 'yan ta da kayar baya
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an samu wata kungiyar 'yan ta'adda da ke kangarar da jama'a bayan jawo su cikinsu
  • An yawan samun kungiyoyin ta'addanci da ke tasowa a nahiyar Afrika, lamarin da ke kara sanya tsoron a zukatan jama'a

Mozambique - Rundunar sojin Mozambique ta ce ta kama wasu tsageru da ke alanta jihadi a yankin kasar, inda suke horar da jama'a kan akidarsu kana wasu 16 sun mutu.

Rahoton BBC Hausa ya ce, mutum hudu aka kama da zargin kafa kungiya haramtacciya tare da yaudarar mutane suna shiga gami da daura su a mummunar hanya.

Bernardino Rafael, kwamandan 'yan sanda a kasar ne ya bayya hakan, inda yace mutane 16 da suka mutu sun mutu ne sakadamakon arangama da sojoji.

Yadda zakuna da kadoji suka yi kaca-kaca da 'yan ta'adda
Zakuna Sun Yi Kaca-Kaca da Wasu ’Yan Ta’adda da Sunan Jihadi a Mozambique | Hoto: allafrica.com
Asali: UGC

A wani yanayi mai ban mamaki, ya kuma ce zakuna da kadajoji ne suka afka ma wasu daga cikin 'yan ta'adda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rafael ya bayyana wadannan maganganu na kamu da hallaka 'yan ta'adda ne a yayin ganawa da mazauna yankin Quissanga a Cabo Delgado ta Arewacin Mozambique.

Sai dai, rahoton ya ce Rafael bai fadi adadin 'yan ta'addan da dabbobin suka kashe ba, duk da tabbacin da ya bayar na gudunmawar dabbobin a hallaka tsagerun.

Kwamandan ya ce hukumomi za su yi kokarin binne tsagerun da ake da gawarwakinsu a hannu, kamar yadda jaridar CNR ta ruwaito.

Sojoji Sun Dira a Maboyar ’Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 3, Sun Kwato Makamai da Harsasai a Kaduna

A wani labarin kuma, jami'an sojin rundunar Operation Forest Sanity sun farmaki maboyar 'yan bindiga a kokarin da suke na kakkabe dazukan Kuriga-Manini-Udawa a hanyar Chikun zuwa Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Laraba 28 ga watan Satumban Leadership ta ruwaito.

Aruwan ya ce, jami'an tsaron sun yi arba da 'yan bindigan, kuma sun tsere da raunukan harbin bindiga yayin da sojoji suka fi karfinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel