Bayan Malamar Islamiyya, An Kona Gawar Mutumin da aka Kashe a Kano

Bayan Malamar Islamiyya, An Kona Gawar Mutumin da aka Kashe a Kano

  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu fusatattun mutane sun kashe Ahmad Dankoli bisa zargin yunƙurin satar babur a Balare, Ajingi
  • Shaidun gani da ito sun ce bayan kashe shi, mutanen da da suka aikata hakan sun ƙwace gawarsa daga hannun jami'an tsaro sun ƙona
  • Da aka tuntubi rundunar rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ba a kai mata rahoto kan lamarin ba tukuna, amma za ta bincika me ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Wasu fusatattun mutane a garin Balare da ke ƙaramar hukumar Ajingi a Jihar Kano sun kashe wani matashi mai suna Ahmad Dankoli bayan sun zarge shi da yunƙurin satar babur.

Shaidun gani da idon sun tabbatar a cewa bayan sun kashe shi, mutanen sun ƙona gawarsa duk da ƙoƙarin jami'an tsaro na dakatar da lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kori mutanen kauyuka 30 a Sokoto, manya sun dauki mataki

Ahmad Dankoli da aka kashe
Ahmad Dankoli da mutane suka kona bayan zargin satar babur. Hoto: Ahmad Dankoli
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tuntubi rundunar 'yan sandan jihar Kano domin neman karin bayani game da abin da ya faru da matakin da suka dauka.

Maganar kansila a Kano

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kansilan mazabar Balare, Malam Shu'aibu Abdulmumin Yalo, ya ce abin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren Lahadi, ranar kasuwar garin.

A cewar Malam Shu'aibu Abdulmumin Yalo, an zargi marigayin da ƙoƙarin satar babur mallakin wani mutum da ya zo cin kasuwa.

Yadda aka kona matashi a Kano

Kansilan ya ce wani mutum ya hango shi yana ƙoƙarin ɗaukar babur ɗin abokinsa, sai ya kama shi. Daga nan jama'a suka taru suka fara dukansa har ya rasu.

Yalo ya ƙara da cewa jami'an tsaro sun isa wurin domin kwantar da tarzoma, amma yawan mutanen da suka taru ya rinjaye su.

Ya bayyana cewa jami'an sun yi nasarar kwace gawar, amma fusatattun matasa suka ƙwace ta daga hannunsu suka banka mata wuta.

Kara karanta wannan

An rike dan ta'adda da ya nufi fadar sarki da bindiga zai kai hari

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Batun yawan satar babur

Da ya ke karin bayani game da lamarin, kansilan ya ce al'ummar yankin na fama da yawaitar satar babura a cikin 'yan watannin nan.

A cewarsa, an samu rahoton sace babura sama da 32 a kasuwar cikin watannin baya, lamarin da ya haddasa fushi da takaicin jama'a.

Ya ce abin ya jefa al'umma cikin firgici, har 'yan kasuwa suka watse daga kasuwar a daren Lahadi, kafin harkoki su koma yadda aka saba a ranar Litinin.

Da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce har zuwa lokacin ba a kai rahoton lamarin ofishinsu ba, amma ya yi alƙawarin bincike kan abin da ya faru.

A wani sako da marigayin ya wallafa a shafinsa na Facebook kafin a kashe shi, mutane da dama na shiga sashen sharhi suna masa addu'ar samun rahama.

An kashe malamar Islamiyya

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu mutane sun taru sun kashe malamar Islamiyya mi suna Ummulkhairi a Maraban Jos a Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka barna a Sokoto, sun kashe basarake, ɗansa da wasu mutane

An kashe malamar ne a lokacin da take kan hanyar zuwa wajen karatu, inda jama'a suka zarge ta da satar yara ba tare da wani dalili ba.

Kisan matar ya dauki hankalin al'umma da dama, inda aka yi kira ga jami'an tsaro su tabbatar sun yi cikakken bincike domin hukunta masu laifin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng