Yadda Bello Turji Ya Sake Sha Da Kyar Daga Barin Bama-Baman Sojin Sama a Jeji

Yadda Bello Turji Ya Sake Sha Da Kyar Daga Barin Bama-Baman Sojin Sama a Jeji

  • Sojojin saman Najeriya sun yi barin-wuta a jejin Fakai inda Bello Turji da wasu mutanensa ke biki
  • Jiragen jami’an tsaron ya hallaka wasu ‘yan bindiga a dajin, amma bai yi nasarar kashe Bello Turji ba
  • A lokacin da aka yi ruwan wuta, Turji ya je yin sallah, bama-baman sun rutsa da wadanda ke wurin

Zamfara - Bayanai sun fito game da yadda Bello Turji ya tsira daga haren-haren bama-baman dakarun sojojin saman Najeriya suka kai masu a jeji.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin cewa jiragen yakin sojojin sama sun rutsa mafakar su Bello Turji a Fakai a karamar hukumar Shinkafi.

Rundunar Sojojin Najeriya sun samu labarin ‘yan bindiga za su taru a garinsu Bello Turji ne domin bikin suna a ranar Asabar, sai aka shirya jirage biyu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin Yaƙin Sojoji Ya Kai Sabon Harin Bama-Bamai Maɓoyar Bello Turji a Zamfara

Rahoton bai iya bayyana irin barnar da wadannan jirage suka yi wa su Bello Turji ba, amma an tabbatar da cewa mafi yawan mutanensa sun kubuta.

Turji sun je sallar azahar

A daf da lokacin da sojoji za su fara barin wuta a dajin, sai Turji ya bar wurin da ake taro da nufin ya yi sallar azahar, wannan ya yi sanadiyyar tsiransa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Shi Turji ya bada umarnin a je ayi salla. Wadanda ba su tafi sallah ba ne bam-bamai suka rutsa da su.”

- Wani 'dan bindiga

Super Tucano
Jiragen Super Tucano Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Karo na biyu da Turji ya tsira

Wannan ne karo na biyu da Turji ya sha da kyar daga irin wannan hari. A karshen shekarar bara, sojojin sun harba masa bam, amma dai ba su dace ba.

Wani daga cikin ‘yan bindigan a kauyen Dangondi, wanda ya tsallake luguden bama-baman, ya shaidawa jaridar cewa an birne wadanda suka hallaka.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: An Kama Wani Kasurgumin Ɗan Bindiga da Sojan Bogi a Jihar Zamfara

Wa ya ankarar da sojoji?

Ana zargin abokan fadan wannan kasurgumin ‘dan bindigan ne suka tona asirinsa a wajen jami’an sojoji domin yana da gungun makiya a kauyen Maniya.

An dade ana rigima tsakanin yaran Turji da mutanen wani ‘dan bindiga a Maniya da ake kira Dullu. Da alamu wannan rikicin ne ya amfani sojojin saman.

Kwanakin baya Turji ya gargadi yaran Dullu su daina tare matafiya da mutanen Maniya domin ya yi sulhun zaman lafiya da 'yan wadannan kauyuka.

'Yan bindiga sun tare malamai

A baya an samu rahoton yadda Shehin malami, Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya yi bayanin abin da ya faru tsakaninsu da ‘yan bindiga a hanyar Nijar.

Wasu miyagun ‘yan bindiga suka tare tawagar malaman a hanyar dawowarsu daga kasar Nijar, amma Ahmad Guruntum yace ba a hallaka kowa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel