Asiri Ya Fara Tonuwa da Sojoji Suka yi Ram da Masu Taimakon 'Yan Garkuwa da Mutane

Asiri Ya Fara Tonuwa da Sojoji Suka yi Ram da Masu Taimakon 'Yan Garkuwa da Mutane

  • Sojoji sun yi nasarar cafke wasu da ake zargi da laifin daukar nauyin ta’adin ‘Yan bindiga a jihar Kaduna
  • ‘Yan rundunar Operation Hadarin Daji sun kama mutane biyu za su cire makudan kudi a wani banki a Zaria
  • Darektan harkokin yada labaran sojoji yace suna neman wanda ake tunanin yana taimakon ‘Yan bindigan

Kaduna - Dakarun Operation Hadarin Daji sun kama wasu mutane biyu da ake zargin suna taimakawa ‘yan bindiga da masu garkuwa da jama'a a Kaduna.

Kamar yadda rahotanni daga Daily Trust da wasu jaridun suka bayyana a ranar Alhamis, an kama wadannan mutane ne a garin Zaria a jihar Kaduna.

Jami’an sojoji sun shaida cewa suna neman wani mutumi mai suna Alhaji Abubakar bisa zargin shi yake ba miyagun ‘yan bindiga taimako na harkar kudi.

Kara karanta wannan

‘Yan damfara Sun yi wa Asusun Bayin Allah Tas a Banki, Sun Sace Naira Miliyan 523

Darektan harkokin yada labarai na gidan soja, Manjo Janar Musa Danmadami ya yi wannan bayani da yake jero nasarorin da sojoji suka samu a Satumba.

Dubu ta cika!

Janar Musa Danmadami yake cewa sojoji sun kama mutanen nan biyu da ke da alaka da Alhaji Abubakar a wani banki da ke PZ a Zaria, za su cire kudi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Premium Times tace sun zo bankin ne za su cire N14,000,000.00 yayin da dubunsu ta cika.

Wani mara gaskiya a daure
Wani mara gaskiya a daure Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A ranar 15 ga watan Satumba mutanen da aka kama suka je bankin domin cire kudin fansa da ake zargin an tura a asusun mutumin da ake neman ido rufe.

Babban jami’in sojan yake cewa jami’an tsaro suna bincike domin a damko wannan mutumi da duk masu hannu wajen taimakawa ‘yan ta’adda a yankin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani Bam Ya Fashe a Babban Birnin Jihar Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta fahimci wannan babban banki da aka ambata yana da rassa biyu a unguwar PZ, zuwa yanzu dai jami’an bankin ba suyi wata magana ba.

Yakin ISWAP da Boko Haram

Kamar yadda sojan ya bayyana, dakarun Operation Hadin kai na cigaba da nasara a kan ‘Yan Boko Haram da ‘yan ta’addan ISWAP a Arewa maso gabas.

Janar Danmadami yace tsakanin wannan lokaci, sojoji sun hallaka Abu Asiya and Abu Ubaida (A Qaid) a yankin Farisu da ke Sheruri a jejin Sambisa.

'Yan Yahoo sun sace N520m

Kun ji labari wasu kwararrun ‘Yan Yahoo-Yahoo sun shafe kwanaki uku suna satar makudan kudi da mutane suka adana a asusun banki a jihar Legas.

Ana haka sai aka ji DSS masu fararen kaya sun roki kungiyar ASUU ta malaman jami’a su koma karantarwarsu domin gudun rashin tsaro ya barke.

Kara karanta wannan

Yadda Bello Turji Ya Sake Sha Da Kyar Daga Barin Bama-Baman Sojin Sama a Jeji

Asali: Legit.ng

Online view pixel