‘Dan Takarar Gwamna Ya Yi Shekara 1 da Bacewa, Har Yau Babu Wanda Ya ji Labarinsa

‘Dan Takarar Gwamna Ya Yi Shekara 1 da Bacewa, Har Yau Babu Wanda Ya ji Labarinsa

  • Obiora Agbasimalo shi ne wanda ya yi wa Labour Party takarar Gwamna a zaben jihar Anambra a 2021
  • Ana tsakiyar yakin kamfe aka nemi ‘dan siyasar aka rasa, har yanzu babu wanda ya ji labarin inda yake
  • Mahaifiyar ‘dan takarar, Dr. Ada Agbasimalo ta fito tayi magana bayan shekara daya da batar-dabon

Anambra - ‘Yanuwan Obiora Agbasimalo sun shiga yanayin zulumi tun bayan bacewar wannan Bawan Allah lokacin ana yakin neman zaben gwamna.

Punch tace Obiora Agbasimalo wanda ya tsaya takarar gwamnan Anambra a karkashin jam’iyyar LP a bara, ya bace ne tun a ranar 18 ga watan Satumba.

Wasu sun yi awon-gaba da Agbasimalo da zai kai ziyara zuwa garin Azia, a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra, har yau babu wanda ya sake ganinsa a fili.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Zabi Gwamnan APC, Ya Bi Shi Babban Aiki a Yakin Zama Shugaban Kasa

Mahaifiyar wannan ta’aliki, Dr. Ada Agbasimalo ta shaidawa manema labarai cewa babu abin da jami’an tsaro suka yi domin gano Obiora Agbasimalo har yau.

Danginsa na neman taimako

Dr. Agbasimalo tace ya kamata su san halin da ‘danuwansu yake ciki, tayi kira ga Sufetan ‘yan sanda, gwamnatin Anambra da kuma LP su kawo masu agaji.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mahaifiyar ‘dan siyasar take fada a cikin karamar murya cewa duk ‘yanuwa sun damu, musamman mai dakin ‘dan takarar da yanzu ta shiga wani yanayi.

Obiora Agbasimalo
‘Dan Takarar Gwamnan LP, Obiora Agbasimalo Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Godwin Agbasimalo ya jawo shi

A cewar tsohuwar, yaron na ta yana aiki a wani banki ne da ke garin Legas, sai ‘danuwan mahaifinsa, Godwin Agbasimalo ya shigo da shi siyasa.

Godwin Agbasimalo wanda aka fi sani da “Oga ndi oga” shi ne ya dauki dawainiyar neman takarar Obiora Agbasimalo a karkashin inuwar Labor Party.

Kara karanta wannan

Baya da kura: Atiku Ya Sheka Kasar Waje, Maganar Shawo Kan Rikicin PDP Ya Wargaje

Kamar yadda Ada Agbasimalo take fada, wani mai suna Chukwudi Odimegwu ake zargin ya kai ‘dan takarar gwamnan wajen wadanda suka dauke shi.

Suna kan hanyarsu ta zuwa Azia daga garin Ezinifite a karamar hukumar Nnewi ta kudu ne dai wannan mummunan abin ya faru a lokacin yakin zabe.

Yanzu fiye da shekara daya kenan ana sauraron dawowar Agbasimalo, amma babu ko duriyarsa. Tuni har an rantsar da sabon gwamna a jihar Anambra.

Shekaru 3 da bacewar Dadiyata

Tun a ranar 1 ga watan Agusta, 2019, wasu mutane biyu da ba a san su wanene su ba, su ka dauke Malam Abubakar Idris wanda aka fi sani da Dadiyata.

Shekaru uku kenan ba a kuma jin inda wannan matashi yake ba. Ana zargin wannan ta'adi ne ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsa a Afrilun 2022.

Kara karanta wannan

Tun Yanzu, Atiku Abubakar Ya Fara Tattara Sunayen Wadanda Zai Ba Mukamai

Asali: Legit.ng

Online view pixel