Sauki Zai Samu: Dangote da Wasu Manyan Dillalai Sun Rage Farashin Litar Fetur

Sauki Zai Samu: Dangote da Wasu Manyan Dillalai Sun Rage Farashin Litar Fetur

  • Matatar Dangote da manyan masu sayar da mai sun sake rage farashin fetur da dizal a matatar mai ranar Litinin saboda sabuwar gasa a kasuwa
  • Ministan Albarkatun Man Fetur ya ce yadda ake samun faduwar danyen mai a kasuwannin duniya, bai kamata farashin fetur ya yi tsada ba
  • Rahoto ya ce gidajen mai da dama a Legas, Port Harcourt, Warri da Calabar sun rage farashin fetur da dizal domin jawo karin abokan hulda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legas - Kasuwar man fetur ta Najeriya ta sake samun saukin farashi a ranar Litinin bayan Matatar Dangote da wasu manyan masu sayar da mai suka rage farashin fetur da dizal a matakin matata.

Rage farashin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun gasa tsakanin masu kasuwancin man fetur, tare da karin wadatar kayayyakin man fetur a kasuwa.

Kara karanta wannan

An fitar da abubuwan da Sarkin Musulmi ya tattauna da wakilan Fafaroma

Dangote da wasu dillai sun rage farashin fetur
Wani mutumi yana sayar da fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dangote ya rage farashin fetur

Kafin sanar da sabon farashin, karamin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya bayyana cewa farashin fetur da ake sayarwa yanzu bai dace da yadda farashin danyen mai ya ragu a kasuwannin duniya ba, in ji rahoton Vanguard.

Ministan ya yi wannan bayani ne a wani taron masu ruwa da tsaki da Hukumar NMDPRA ta shirya, wanda ya samu halartar wakilan Matatar Dangote, MEMAN, IPMAN, DAPPMAN, NARTO da PETROAN.

Sabon rahoton farashin matatun mai ya nuna cewa Matatar Dangote ta rage farashin fetur a Legas da N3 kan kowace lita, daga N1,079 zuwa N1,076, yayin da ta bar farashin dizal a N1,500 kan kowace lita.

'Yan kasuwa sun rage farashin fetur

Sauran manyan masu kasuwancin mai su ma sun bi sahu. NIPCO ta rage farashin fetur da N2 zuwa N1,076, yayin da Pinnacle ta rage da N3 zuwa N1,075 kan kowace lita.

Kamfanonin Sahara, AIPEC da African Terminal su ma sun rage farashinsu da N4, inda suka daidaita litar kan N1,075, yayin da Aiteo ta ci gaba da sayar da fetur a N1,075 ba tare da wani sauyi ba.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa mai ya sauka a duniya amma Dangote bai karya kudin fetur ba

A bangaren dizal, Rain Oil ta rage farashinta da N15 zuwa N1,430 kan kowace lita. Ibeto, Duport da Ibachem su ma sun daidaita farashinsu zuwa N1,430, yayin da Dangote ya ci gaba da sayar da dizal a kan N1,500.

Karin kamfanoni sun rage kudin dizal

A Port Harcourt, Matrix ta rage farashin fetur da Naira takwas zuwa N1,087, sannan ta rage dizal da Naira 55 zuwa N1,465, wanda shi ne mafi girman saukin farashin dizal da aka samu a ranar.

An samu sauki kudin fetur da dizal a Najeriya
Wani mutumi ya na zuba fetur a cikin wata mota a gidan mai. Getty Images
Source: Getty Images

Sigmund ta rage farashin fetur da Naira 12 zuwa N1,082, amma ta kara farashin dizal da Naira biyu zuwa N1,463, a cewar rahoton Punch.

Haka kuma a Calabar da Warri, wasu kamfanoni sun rage farashin fetur da dizal domin ci gaba da yin gogayya a kasuwa.

Masana na ganin cewa idan wannan yanayi ya ci gaba, masu amfani da man fetur za su iya samun karin saukin farashi a gidajen mai a kwanaki masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com