Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Sheke Manoma 3, Sun yi Garkuwa da Wasu 22

Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Sheke Manoma 3, Sun yi Garkuwa da Wasu 22

  • Miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki wasu kauyukan karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna inda suka tafka barna
  • Maharan sun halaka manoma uku da suka tarar suna ayyuka a gonakinsu tare dfa yin awon gaba da wasu mutum 22
  • Ba su tsaya nan ba, sun kwacewa mutane babura tare da balle shaguna inda suka wawushe kayayyakin jama'a

Kaduna - Wasu ‘yan bindiga da suka kai farmaki a wasu kauyukan karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna sun halaka a kalla mutane uku.

Channels TV ta rahoto cewa, an ce wadanda harin ya ritsa da su manoma ne da ke aiki a gonakinsu ranar Asabar lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmakin.

Taswirar Kaduna
Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Sheke Manoma 3, Sun yi Garkuwa da Wasu 22. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Duk da yake har yanzu hukumomin tsaro ba su tabbatar da farmakin ba, shugaban kungiyar ci gaba ta masarautar Birnin-Gwari, Ishaq Kasai, ya ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutane 22 tare da kwace babura.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari Kan Bayin Allah, Sun Kashe Rayuka

Kamar yadda yace, wurin misalin karfe 7 na yammacin ranar Asabar, 24 ga watan Satumba, ‘yan bindigar sun kai farmaki garin Hayin Gada da ke unguwar Damari a unguwar Kazage, inda suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da mutane 12.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Har ila yau, sun yi awon gaba da kayayyakin cikin shaguna a unguwarsu yayin harin.

A wani labarin kuwa, duk a wannan rana, wasu gungun ‘yan bindiga sun kai hari wata gona da ke kan titin Birnin-Gwari zuwa Kaduna, inda suka halaka mutum daya sannan suka tafi da mutum shida.

‘Yan bindigar sun kara yin garkuwa da wasu mutane hudu a Dajin Jangali tare da kwace babura uku daga hannun manoma a unguwar Kamfanin Doka.

A halin da ake ciki, kungiyar ci gaba ta Masarautar Birnin-Gwari ta shiga matukar damuwa kan yadda ‘yan ta’adda ke ci gaba da mamaye yankuna daban-daban tare da wawure kayayyaki a shaguna ba tare da fuskantar kalubale ba daga jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan Lantarki Sun Yi Barazanar Kashe Wutan Najeriya Gaba Daya

Kungiyar ta kuma yi kira ga hukumomin da ke da ruwa da tsaki da su kara kaimi wajen yakar ayyukan ta’addanci a karamar hukumar Birnin-Gwari musamman a wannan lokaci na noma.

A zantawar da Legit.ng tayi da Malam Magaji Bello, mazaunin kauyen Gamji dake da kusanci da Birnin Gwari, ya bayyana yadda 'yan bindigan suka halaka dan'uwansa, daya daga cikin manoman da suka kashe a farmaki.

"Abun akwai tashin hankali da bada tsoro. Malam Ya'u ya rasa ransa yayin da yake gona inda 'yan bindiga suka kai musu farmaki. A halin yanzu dar-dar manoma ne zuwa gonakinsu hatta a nan Gamji.
"A wasu kauyukan kuwa, sun biya wasu kudade na harajin da suka kallafa musu kuma sun yi yarjejeniyar zaman lafiya inda ba su kai musu hari.
"Allah ya gafartawa Ya'u, ya karba shahadarsa. Muna kira ga gwamnati da ta dauka mataki tun kafin su halaka dukkanmu. Don a baya can kake jin irin wannan labarin, yanzu kuwa ga shi ya iso gida za a ce."

Kara karanta wannan

Tashin hankali a wata jihar Arewa yayin da 'yan sanda suka kashe matashi dan shekara 16

- Malam Magaji yace.

Borno: Zulum Ya Sanar da Abun Mamakin da Ya Faru da 'Yan Ta'adda Wanda Ba a Taba ba a Duniya

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, yace sama da mambobin Boko Haram da ISWAP 90,000 ne suka mika ga hukuma cikin shekara daya.

Gwamnan yayin da yake jawabi a taron majalisar dinkin duniya karo na 77 da aka yi a New York, yace ‘yan ta’adda da kansu suka dinga mika wuya wurin sojoji, jaridar TheCable ta rahoto hakan.

Zulum yace wannan bai taba faruwa ba a ko ina a duniya kuma yanzu ta’addanci na zuwa karshe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel