Gwamnoni 4 na Najeriya da Nijar Sun yi Muhimmiyar Ganawa a Maradi

Gwamnoni 4 na Najeriya da Nijar Sun yi Muhimmiyar Ganawa a Maradi

  • Gwamnonin jihohi hudu na Najeriya da suka hada da Zamfara, Sokoto, Katsina da Kebbi sun gana da Gwamnan Maradi na Nijar
  • Sun tattauna ne lkan yadda zasu kawo karshen rashin tsaro da ta'addanci da ya addabi yankin har yanzu
  • Sun tabbatar da cewa zasu aiwatar da abubuwan da suka tattauna a kai domin tabbatar da tsaro a yankunansu

Gwamnonin jihohin Najeriya hudu da ke kan iyakar Najeriya da Nijar sun gana a Katsina da gwamnan Maradi a jamhuriyar Nijar domin tsara wata hanyar yaki da matsalar tsaro da ke addabar yankunan, Daily Trust ta rahoto.

Taswirar Katsina
Gwamnoni 4 na Najeriya da Nijar Sun yi Muhimmiyar Ganawa a Katsina. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A taron tsaro da aka yi na kwana daya a garin Maradi, gwamnonin Katsina, Aminu Bello Masari; Aminu Waziri Tambual (Sokoto) da kuma mataimakan gwamnonin Zamfara da Kebbi, duk sum hallarta.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Nemi Buhari Ya Tsige Gwamnan CBN Daga Wani Babban Mukami

An kara da gayyatar shugabannin gargajiya da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a taron da aka yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamna Schiabou Aboubacar na Maradi wanda ya bayyana bude taron, ya ce za a samar da hanyoyin magance matsalolin tsaro a yankin Sahel baki daya.

A nasa jawabin, Gwamna Masari na jihar Katsina ya ce gwamnatin jihar na yin duk mai yiwuwa don magance matsalar rashin tsaro, musamman a matakin jiha.

Ya ce gwamnatin jihar ta tabbatar da kwarin gwiwa ga sarakunan gargajiya da masu rike da kananan hukumomi don tunkarar matsalolin da ke kunno kai a yankunansu.

A jawabansu na daban, sauran gwamnonin sun bayyana kwarin guiwarsu kan taron da aka yi tsakanin bangarorin biyu tare da yin alkawarin aiwatar da sakamakonsa babu jimawa.

Babu Wata Jiha da Aka Ba Izinin Mallakar Makamai Masu Sarrafa Kansu, Martanin Fadar Buhari Ga Gwamna Akeredolu

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaba Buhari ya bayyana yadda sabbin shugabannin za su samu

A wani labari na daban, Gwamnatin Najeriya ta ce, babu wata jiha a Najeriya da ke da ikon mallakar makamai masu sarrafa kansu kamar dai bindigogi kirar AK47, TheCable ta ruwaito.

Wannan batu na fitowa ne daga wata sanarwa da fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fitar a yau Talata 27 ga watan Satumba.

Gwamnati ta ce, mallakar bindiga kirar AK47 matukar ba a hannun jami'an tsaro bane to tabbas ya saba doka, kuma akwai hukunci a kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel