Annoba ta Barke a Sansanin Tsoffin 'Yan Boko Haram, Wasu Sun Fara Shekawa Lahira
- Gwamnatin jihar Borno ta sanar da mutuwar mutum biyu daga cikin tubabbun 'yan Boko Haram sakamakon annobar amai da gudawa
- Sai da mazauna sansanin sun tabbatar da cewa rayuka 20 aka rasa daga ranar Juma'a zuwa Asabar bayan annonar ta barke
- Kwamishinan harkokin mata da cigaba, Zuwaira Gambo, tace an kwashe wadanda suka kamu da cutar kuma an killace ana musu magani
Borno - A kalla mutum biyu sun sheka lahira bayan annobar amai da gudawa ta barke a sansanin tsofaffin mayakan Boko Haram dake garin Maiduguri a jihar Borno.
Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da mutuwar a sansanin Kosheri dake kan titin Maiduguri zuwa Dikwa. Gwamnati tace da yawa daga cikin mazauna sansanin basu da lafiya kuma ana kula da su da magunguna.

Asali: UGC
Wata majiya daga sansanin ta sanar da Premium Times cewa, an rasa rayuka kusan 20 a wurin sakamakon annobar.
"Zan iya tabbatar muku da cewa annobar ta barke tun daga ranar Juma'a kuma mutum 14 sun rasa rayukansu."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
- Majiyar tace kamar yadda ma'aikacin lafiya ya tabbatar mata.
Majiyar wacce ta bukaci a boye sunanta saboda tsaro, tace wasu mutum shida sun sake mutuwa a ranar Asabar.
Sai dai, a martanin ranar Lahadi, gwamnatin jihar Brono tace rayuka biyu aka rasa a sansanin.
"Rayuka biyu kadai aka rasa bayan barkewar annobar amai da gudawa a sansanin Kosheri."
- Kwamishinan harkokin mata da cigaba, Zuwaira Gambo ta sanar da Premium Times a ranar Asabar.
“Sauran wadanda aka gano suna dauke da cutar an kwashe su daga sansanin tare da kai su inda za a killace."
Har a halin yanzu dai ba a fitar da sunayen wadanda suka rasa rayukansu ba a sansanin.
Duk da ba a samu jami'ai daga ma'aikatar lafiya ba domin tsokaci kan lamarin, kwamishinan harkokin matan tace:
"Duk wanda lamarin ya shafa a ma'aikatar lafiya ya je ya duba halin da sansanin yake ciki."
Sojojin Sama Sun Yi Luguden Wuta A Sansanin Gogarman Yan Bindiga Bello Turji
A wani labari na daban, 'yan bindiga masu tarin yawa na sansanin fitaccen ‘dan ta’adda Bello Turji, sun sheka lahira, jaridar PR Nigeria ta rahoto.
An halaka ‘yan ta’addan ne a wani samamen ba-zata da dakarun sojin rundunar Operation Forest Sanity suka kai dazukan Zamfara.
Harin ba-zatan an yi shi ne da jiragen yakin sojin sama bayan sun samu bayanan sirri.
Asali: Legit.ng