"Yadda Dogo Gide Ya Sace Yarinta Mai Shekara 16 a Makaranta, Ya Aurar da Ita"

"Yadda Dogo Gide Ya Sace Yarinta Mai Shekara 16 a Makaranta, Ya Aurar da Ita"

  • Sani Kaoje ya bada labarin yadda suka yi fama bayan ‘yan bindiga sun shiga makarantar FGC Yauri
  • Diyar Alhaji Sani Kaoje tana cikin yaran da su Dogo Gide suka yi garkuwa da su, har yau suna nan a tsare
  • ‘Dan ta’addan ya nunawa mahaifinta cewa ya aurar da Farida Kaoje tun da an ki biyan kudin fansarta

Kebbi - Sani Kaoje mai shekara 66 a Duniya, mahaifi Farida Kaoje ne, wanda tana cikin ‘yan makarantar gwamnati da aka sace a garin Yauri.

A wata hira ta musamman da ya yi da Premium Times, Alhaji Sani Kaoje ya shaidawa Duniya Dogo Gide ya aurar masa da ‘yar da ya haifa.

Farida Kaoje mai shekara 16 a Duniya, tana cikin yaran da wannan gawurtaccen ‘dan bindiga ya aurar bayan an yi garkuwa da su tun a Yunin 2021.

Kara karanta wannan

Hauhawar Farashin Kaya: Gwamnatin Buhari Na Shirin Karawa Ma’aikata Albashi

Kamar yadda mahaifin ya fadawa jaridar, ‘ya ‘yansa 19 da mata uku, kuma Farida ita ce ta 15 a gidan. A lokacin da aka dauke yarinyar, shekararta 15.

Mahaifiyar Farida ta kawo mani labari

“Ina kalaci wata rana da safe, sai mahaifiyar Farida ta auko dakina, ta fada mani, ta ji labarin an shiga FGC Birnin Yauri, an sace yaran makaranta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai na ruga zuwa makarantar, na iske sauran iyaye. Da farko shugabannin makarantar sun hana mu shiga, sai da suka tabbatar muna da ‘ya ‘ya.
Dogo Gide
Farida Kaoje Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Baba an yi awon-gaba da mu!

Sa’a guda bayan an dauke su, Farida ta kira ni da lambar wayar kawarta. Ta fada mani “Baba an yi gaba da mu, ana shiga da mu wani jeji a Zamfara.”

- Alhaji Sani Kaoje

Mahaifin budurwar yace ya kwantar mata da hankali, ya yi mata addu’ar Ubangiji ya kare su daga hannun miyagu. Tun lokacin, iyakar maganarsu kenan.

Kara karanta wannan

Yadda ‘Dan China Ya Yaudari Ummita a Kan Shiga Musulunci inji Babbar Kawar Ummita

Aurar da Farida

An tambayi Sani Kaoje ta ya san da an aurar da ‘yarsa bayan an gagara biyan N100m zuwa N50m da ‘yan ta’addan suka nema daga hannun gwamnati.

Ga amsar shi:

“Shi da kan shi (Dogo) ya fada mani a wayar salula. Dogo Gide ya san Yauri da kyau, domin ya taba zama a nan. Da kan shi ya fada mani ya aurar da ita.
Sai dai bai fito bara-baro ba, ya yi magana mai harshen damo, yana cewa ya aurar da sauran yara 10. A game da Farida, sai yace yana kula da ita da kyau.
Bai fito kai-tsaye ba, amma ya fada mani ko da na mutu, akwai wadanda su za su gaji Farida daga gidana, yana dai nufin ya aurar da ita kawai.

- Alhaji Sani Kaoje

Tun da gwamnati ta ki biyawa ‘yan ta’addan bukatunsu domin a fito da yaran, tsohon ma'aikacin gwamnatin ya mika lamarinsa ga Allah, domin bai da hali.

Kara karanta wannan

Yadda saurayin diyata dan China ya shiga har gida ya caccaka mata wuka, inji mahaifiyar Ummita

Iyaye sun hakura

Watanni kadan bayan abin ya faru, sai aka ji labari iyayen daliban kwalejin tarayya ta Birnin Yauri a jihar Kebbi sun ce sun cire ransu daga gwamnati.

Iyayen sun bayyana alhininsu kan yadda 'ya'yansu suka dauki kwanaki masu tsawo a hannun miyagu. Har yau dai wasu yaran ba su dawo gidajensy ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel