Yan ta'adda
An kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a wani yankin jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas. An bayyana yadda aka yi ya shiga hannun jami'an 'yan sanda.
Rundunar Tsaro a Najeriya ta nemi hadin kan al'umma wurin yakar ta'addanci a kasar, rundunar ta ce ita kadai ba za ta iya kawo karshen matsalar tsaro ba.
Daya daga cikin 'yan matan Dapchi da kungiyar Boko Haram su ka kama, Leah Sharibu yanzu ita ke jagorantar tawagar kula da lafiyar mayakan a yankin Tafkin Chadi.
Rundunar sojin Najeriya ta yi ajalin kasurgumin kwamandan kungiyar Boko Haram, Ari Ghana a Borno yayin kai wani farmaki da su ka yi a karamar hukumar Gwoza.
Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai wani mummunan hari kan matafiya a jihar Borni inda suka salwantar da rayukan bayin Allah masu yawa ciki har da jami'in soja.
Rundunar ƴan sandan jihar Taraba ta samu nasarar cafke miyagun ƴan ta'adda masu ɗumbin yawa waɗanda ake zargi da aikata laifin garkuwa da mutane.
Dakarun sojojin Najeriya sun murkushe wasu tsagerun yan ta'adda 52 a fadin kasar nan. Sun kuma yi nasarar ceto mutane 62 da aka yi garkuwa da su.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a jihar Kogi inda suka yi awon gaba da wani babban likita. Ƴan bindigan sun kira waya sun nemi a ba su maƙudan kuɗin fansa.
Hare-haren ƴan bindiga na ƙara yawaita a jihar Bauchi wanda hakan ya sanya aka ɗauki matakin magance matsalar ta hanyar shigar da mafarauta cikin yaƙin.
Yan ta'adda
Samu kari