Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Mata Biyar Jami'ar FUDMA a Jihar Katsina

Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Mata Biyar Jami'ar FUDMA a Jihar Katsina

  • Ƴan bindiga sun kai hari a ɗakunan kwanan ɗalibai na jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma (FUDMA) a jihar Katsina
  • Ƴan bindiga sun yi awon gaba da ɗalibai mata guda biyar a yayin harin da suka jkai a ɗakunan kwanan da ke a wajen makaranta
  • Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin inda suka ƙara da cewa an cafke wani mutum ɗaya bisa zargin ba ƴan bindigan bayanai

Jihar Katsina - Wasu miyagu ɗauke da makamai da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne, sun kai farmaki a ɗakunan kwanan ɗalibai na jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma (FUDMA) a jihar Katsina.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a yayin harin, ƴan bindigan sun yi awon gaba da ɗalibai mata na jami'ar guda biyar.

Yan bindiga sun sace daliban FUDMA
Yan bindiga sun sace dalibai mata a FUDMA
Asali: Twitter

Yadda ƴan bindigan suka sace ɗaliban

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Babban Kusan Gwamnati

Lamarin ya auku ne a daren ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba, a ɗakunan kwanan ɗalibai na wajen makaranta da ke bayan makarantar Mariamoh Ajiri, kusa da kasuwar Laraba a Dutsinma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ɗalibi da ke karatu a jami'ar ya bayyana cewa:

"Biyar daga cikin ɗaliban da aka yi garkuwa da su, sun fito ne daga jihohin Kano da Nasarawa, kuma biyu daga cikinsu suna shekarar ƙarshe ne a jami'ar."

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, babu wani bayani dangane da halin da ɗaliban ke ciki, domin waɗanda suka yi garkuwa da su ba su tuntubi iyalansu ba.

Ɗalibai sun tabbatar da cewa sakamakon wani abu makamancin haka da ya faru a jami'ar tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara, hukumar ta FUDMA ta umurci dukkan daliban da su dai na fitowa waje daga ƙarfe 10 na dare.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Jami'ar Usmanu DanFodiyo? VC Ya Yi Karin Haske

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar harin

Shugaban sashin hulda da jama'a na jami'ar Habibu Umar Aminu ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na daren ranar Laraba, inda ya ƙara da cewa ana cigaba da ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Sadiq Aliyu Abubakar, ya ce an kama mutum ɗaya da ake zargi da bayar da bayanai ga ƴan bindigan.

Ya bayyana cewa an kuma kama wasu mutane da ake zargin suna da hannu wajen yin garkuwa da ɗaliban, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Aliyu ya ci gaba da cewa, jami'an tsaro sun yi haɗin gwiwa domin ceto daliban ba tare da ko ƙwarzane ba.

Yan Bindiga Sun Halaka Kansila a Katsina

A wani labarin kuma, wasu ƴan miyagun sun kai farmaki a garin Funtua na jihar Katsina, inda suka halaka mutum ɗaya.

Mutumin da ƴan bindigan suka. Halaka shi ne kansilan mazabar Nasarawa a Funtua wanda yana daga cikin masu aikin sintirin samar da tsaro cikin dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel