Duban Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane Ta Cika, an Damke Shi a Jihar Yobe

Duban Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane Ta Cika, an Damke Shi a Jihar Yobe

  • 'Yan sanda a jihar Yobe sun yi nasarar kame wani wanda ake zargi da aikata munanan ayyukan ta'addanci
  • Ana zargin Mohammed Wada da kitsa ayyukan ta'addanci da garkuwa da mutane a jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas
  • Jihohin Arewacin Najeriya na yawan fama da barnar masu garkuwa da mutane, musamman Arewa maso Gabas da Yamma

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Yobe - Jami’an ‘yan sanda sun kama shugaban wata tawagar masu garkuwa da mutane da neman kudin fansa a Damagum da ke Kolere da wasu sassan Tarmuwa da Dapchi a jihar Yobe.

An kama Mohammed Wada mai shekaru 35 dan kauyen Kanda ne a karamar hukumar Fune a unguwar Kolere da ke garin Fune, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan labari dai na fitowa ne daga rundunar 'yan sandan jihar, inda suka bayyana yadda aka kama tsagean.

Kara karanta wannan

Yadda aka kamo wasu mutum 5 da suka yunkurin siyar da jariri mai kwanaki 8 a Kano

An kama kasurgumin mai garkuwa da mutane
An kama mai garkuwa da mutane a Yobe | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, ya ce an kama wanda ake zargin dauke da babbar bindiga, kananan bindigu guda biyu da wasu harsasai a wani samame da suka kai a dajin Kyari Ngaruhu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dan ta'adda ya amsa lafinsa

Abdulkarim ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin kitsawa tare da aikata ta’addanci da dama a yankunan jihar, Daily Post ta tattaro.

Hakazalika, ya ba da misali da wasu abubuwa guda biyu da aka samu a wurin tsagran da suka hada da N2.5m da N5m da ya karba a matsayin kudin fansa daga wadanda da ya sace.

Arewacin Najeriya na yawan fuskantar barnar masu garkuwa da mutane da kuma karbar kudin fansa.

Musamman jihar Yobe, tana daga cikin jihohin da barnar Boko Haram ta shafa tun farkon fara ayyukan ta'addanci da sunan jihadi a Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Wike ya kori manyan jami'an hukumomi da kamfanonin FCTA

Daga zuwa garkuwa da makwabcinsa aka harbe shi

A wani labarin na daban kuma, matashi ne ya hadu da tsautsayi yayin da yi niyyar yin garkuwa da makwabcinshi a jihar Neja.

Matashin mai suna Isma'ila ya hadu da harbin bindiga inda ya tara gungun masu garkuwan don sace makwabcinshi.

'Yan bindigan sun kai farmakin ne gidan Alhaji Mohammed Makasudi da ke Sabon Wuse da ke karamar hukumar Tafa da ke jihar, cewar Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel