Yan Bindiga Sun Sace Wani Babban Likita a Jihar Kogi

Yan Bindiga Sun Sace Wani Babban Likita a Jihar Kogi

  • Ƴan bindiga sun yi awon gaba da darektan asibitin Victory Hospital da ke a Ogaminana a jihar Kogi
  • Ƴan bindigan sun yi awon gaba Dr. Austin Uwumagbe ne a bayan ya tashi daga wajen aikinsa a ranar Talata
  • Ƙungiyar likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar Kogi, ta tabbatar da sace likitan inda ta buƙaci jami'an tsaro da su gaggauta ceto shi

Jihar Kogi - Wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wani likita, Austin Uwumagbe, darektan asibitin Victory Hospital da ke Ogaminana, a ƙaramar hukumar Adavi ta jihar Kogi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an yi wa Dr Uwumagbe ganin ƙarshe ne a ranar Talata bayan ya tashi daga wajen aiki ya nufi gida.

Yan bindiga sun sace likita a jihar Kogi
Yan bindiga sun sace babban likita a jihar Kogi Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Wata majiya daga asibitin ta ce waɗanda suka yi garkuwa da shi sun tuntubi iyalansa, inda suka bukaci a ba su maƙudan kuɗaɗe kafin ya shaƙi iskar ƴanci.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Yanke Hukunci a Kotunan Zabe, Ɗan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

Yadda ƴan bindiga suka sace likitan

Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar Kogi ta tabbatar da sace Dr Uwumagbe a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a, 22 ga watan Satumba, a birnin Lokoja, babban birnin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa mai ɗauke da sa hannun shugaban NMA na jihar, Dakta Baoku Olusola, da sakatare, Dakta Emmanuel Bola Jonah, sun ce an yi garkuwa da abokin aikin nasu ne jim kaɗan bayan ya bar asibitinsa a ranar Talata.

Ƙungiyar a cikin sanarwar ta bayyana cewa:

"An sace shi ne da motar sa, wata kalar toka ƙirar Peugeot 406 mai lamba DAV 561 AA, da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Talata."

Ƙungiyar NMA ta yi Allah wadai da wannan aika-aika tare da neman a gaggauta sakin mambansu da aka yi garkuwa da shi, sannan ta yi kira ga jami’an tsaro da su dauki matakin gaggawa domin ganin likitan ya samu ƴancinsa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da 'Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Babban Malami da Wasu 2 a Babban Birnin Jihar APC

Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka jami'an tsaron rundunar Edo State Security Network da ke ƙarƙashin gwamnatin jihar ranar Alhamis da daddare.

Ƴan bindigan sun harbe jami'an tsaron su uku a yankin Okhun da ke ƙaramar hukumar Ovia ta Arewa maso Yamma a jihar Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel