Dakarun Sojoji Sun Sheke Yan Ta’adda 52, Sun Ceto Mutum 62 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Dakarun Sojoji Sun Sheke Yan Ta’adda 52, Sun Ceto Mutum 62 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kwato makamai da sauran kayayyakin aikata barna a fadin kasar
  • Sojojin sun kuma halaka yan ta'adda 52 tare da kama miyagu 53 da barayin mai guda bakwai
  • Har ila yau, sojojin sun kuma yi nasarar ceto mutane 62 da aka yi garkuwa da su

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Hedkwatar tsaro ta bayyana cewa dakarun sojoji a fadin kasar sun kashe yan ta'adda 52, sun kama miyagu 53, barayin mai guda bakwai da kuma ceto mutane 62 da aka yi garkuwa da su a cikin mako guda.

Darakta mai kula da fannin yada labarai na tsaro, Maj.-Gen. Edward Buba, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ya ce dakarun sojin sun kwato makamai 77 da alburusai iri-iri guda 658, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Miyagu Sun Buɗe Wuta Yayin da Suka Kai Mummunan Hari Gidan Babban Jigon Siyasa a Arewa, Sun Tafka Ɓarna

Dakarun sojoji
Dakarun Sojoji Sun Sheke Yan Ta’adda 52, Sun Ceto Mutum 62 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Hoto: Defence Headquarters Nigeria
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto, Buba ya kuma bayyana cewa yan ta'adda bakwai sun mika wuya ga dakarun sojin cikin wannan lokaci.

Dakarun sojoji sun kama barayin mai da sauransu

Sojojin sun kuma kwato kayayyakin sata da darajarsu ya kai naira miliyan 946.3 daga barayin man.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce ayyukan dakarun a kudu maso kudu ya yi sanadiyar kwato lita 496,250 na dayan mai da aka sace, lita 83,400 na AGO, lita 1,200 na man fetur, injin jan mai guda hutu.

Sauran abubuwan da aka kwato sun hada da jiragen ruwa masu gudu guda biyar, rijiyar mai 34, tankunan ajiya 57, kwale-kwale na katako guda 16, da injina guda uku.

"Gaba daya, a zuwa ranar 22 ga watan Satumban 2023, rundunar sojin sun kashe yan ta'adda 52 sannan sun kama masu laifi 53, barayin mai bakwai yayin da suka ceto mutum 61 da aka yi garkuwa da su. Bugu da kari, yan ta'adda bakwai da suka hada da maza manya biyar da mace babba daya suka mika wuya ga dakarun soji."

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Fashe Da Kuka Wiwi Yayin da Saurayi Ya Yi Mata Korar Kare Daga Gidansa a Bidiyo

Sojoji sun kashe yan bindiga 5, sun ceto wasu dalibai da aka sace a Zamfara

A wani labarin mun ji cewa dakarun sojojin Operation HADARIN DAJI da ke yaki da ta'addanci a yankin arewa maso yamma sun yi nasarar halaka yan bindiga biyar a jihar Zamfara.

Kamar yadda Zagazola Makama ya rahoto, sojojin sun kuma ceto wasu daliban jami'ar tarayya ta Gusau da yan bindiga suka yi garkuwa da su a safiyar ranar Juma'a, 22 ga watan Satumba, a garin Sabon Gida da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel