‘Yan Boko Haram Sun Yi Kashe-Kashe, Sun Dauke Wasu Sarakuna a Jihar Borno

‘Yan Boko Haram Sun Yi Kashe-Kashe, Sun Dauke Wasu Sarakuna a Jihar Borno

  • An hallaka Bayin Allah a hare-haren Boko Haram a wasu kauyukan da ke kudancin Jihar Borno
  • ‘Yan ta’addan sun dauke wasu sarakuna biyu a Burum bayan sojoji sun lallasa su kwanakin baya
  • Mayakan Boko Haram sun kai harin ne domin maida martani ga mutanen da su ka tona masu asiri

Borno - Akalla mutane biyu aka samu labarin mutuwarsu yayin da aka yi awon gaba da wasu mutane shida a wani harin Boko Haram.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa ‘yan ta’addan kungiyar ISWAP sun addabi mutanen yankin Kudancin jihar Borno a ‘yan kwanakin nan.

Lamarin ya kai an dauke sarakunan gargajiya biyu a karamar hukumar Damboa, zuwa yanzu babu labarin inda aka kai manyan kasar.

‘Yan Boko Haram
Sojoji su na yaki da Boko Haram Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Boko Haram a Burum

‘Yan ta’addan sun kai hari a wani kauye mai suna Burum wanda yake kilomita 20 daga hanyar Damboa/Biu a jihar ta Arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Abun Tausayi: Mata da Miji da 'Ya'yansu Sun Mutu Sakamakon Wutar Lantarki Mai Ƙarfi a Jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin a sace sarakunan, dakaru sun yi nasarar hallaka wasu mayakan ‘yan ta’addan da-dama, hakan ya faru a ranar Alhamis da ta wuce.

Wata majiya mai karfi ta shaida mayakan ISWAP sun koma kauyen, su ka dauke mutane a matsayin ramuwar duka abin da aka yi masu.

‘Yan ta’addan da aka fi sani da Boko Haram sun zargi mazauna kauyen da fallasa asirinsu ga jami’an tsaro, har aka iya hallaka sojojinsu.

An dauke Sarakuna da karfin tsiya

"Da karfi da yaji su ka dauke sarakunan gargajiya biyu (Wakilin Lawan da kuma Bulaman kauyen Burum).
Kwanaki hudu kenan, mun damu sosai game da halin da su ke ciki da mummunan yanayin da aka samu kai ciki.

Kamar yadda jaridar ta fitar da rahoto a makon nan, tun da aka dauke mai gari da lawallin, har zuwa yanzu ba a sake jin labarin duriyarsu ba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Ƙara Kashe Mutane a Jihar Sakkwato, 'Yan Sa'kai Sun Fusata Sun Ɗauki Fansa

An yi kira ga gwamnatin Borno

Majiyar ta bayyana cewa su na rokon gwamnati ta sa baki domin a kubutar da sarakunan.

A garuruwan Mugule da Azir, ‘yan ta’addan sun harbe mutane; wasu sun mutu yayin da wasu su ke cigaba da jinya yanzu haka a gadon asibiti.

Yaki da ta'addanci a Arewa

Jagororin musulunci da na Fulani makiyaya sun nuna rashin jin dadinsu da takaici kan yadda aka raba gudumuwar da Remi Tinubu ta bada.

Duk da an kashe musulami a fadan addini a Filato, gwamnati ta zabi kiristoci zalla domin raba masu tallafin uwargidar shugaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel