Yan ta'adda
An kubutar da mutane biyu da aka yi garkuwa da su a ranar Lahadi bayan wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Guto da ke Bwari a babban birnin tarayya Abuja.
Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun samu nasarar tarwatsa barayin man fetur a jihar Rivers. Sojojin sun kuma hallaka 'yan ta'adda a jihar Neja.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da harin kunar bakin wake sa 'yan ta'adda suka kai a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno inda suka hallaka mutane.
Adadin mutanen da suka rasu sakamakon tayar da bama-bamai a jihar Borno ya karu. Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar ta ce an rasa rayukan mutum 18.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wata 'yar kunan bakin wake ta tayar da bam yayin da ake zaman makoki a karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno a Arewa maso Gabas.
A lokacin da ake tunani an fara shawo kan matsalar tsaro a Arewa maso gabas, an kai mugun hari. Rahotanni sun tabbatar da tashin abin da ake tunani bam.
Jami’an hukumar FCCPC sun abka babbar kasuwar sayar da abinci ta Oseokwodu da ke garin Onitsha domin gano dalilan da suka sa farashin kayan abinci ya yi kamari.
Hedkwatar tsara ta kasa (DHQ) ta bayyana nasarar da dakarun sojojin Najeriya suka samu kan 'yan ta'adda daga watan Afirilu zuwa watan Yunin shekarar 2024.
Da misalin karfe 9 na daren ranar Laraba aka ruwaito 'yan bindiga sun farmaki ofishin'yan sanda da ke jihar Ebonyi, kuma har an kashe mutane biyar.
Yan ta'adda
Samu kari