Zamfara: Rashin Tsaro Ya Zo Ƙarshe Bayan Tinubu Ya Ba da Umarni, Ya Yi Kus-kus da Gwamna

Zamfara: Rashin Tsaro Ya Zo Ƙarshe Bayan Tinubu Ya Ba da Umarni, Ya Yi Kus-kus da Gwamna

  • Shugaban Bola Tinubu ya gana da Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara kan matsalolin tsaro a jihar
  • Tinubu ya bukaci gwamnan ya rinka ba shi bayanai lokaci bayan lokaci domin dakile matsalar gaba ɗaya a jihar
  • Kakakin gwamnan, Suleiman Bala Idris shi ya tabbatar da haka inda ya ce Tinubu ya damu da matsalar Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi jihar Zamfara.

Tinubu ya kuma umarci kara tura jami'an tsaro jihar domin tabbatar da kawo karshen matsalar da gaggawa, cewar rahoton Premium Times.

Tinubu ya ba da sabon umarni kan matsalar jihar Zamfara
Shugaban Tinubu ya bukaci samun bayanai daga Gwamna Dauda Lawal na Zamfara kan matsalar tsaro. Hoto: Dauda Lawal Dare, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Alkwarin da Tinubu ya yi wa Dauda

Kara karanta wannan

Minista ya fadi abin da Tinubu ke bukata kaɗai daga 'yan Najeriya domin inganta kasar

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan Zamfara, Suleiman Bala Idris ya fitar a ranar Juma'a 12 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bala ya ce Tinubu ya ba Gwamna Dauda Lawal tabbacin dakile matsalar tsaron da ta addabi jihar baki daya, kamar yadda Arise TV ta tattaro.

Ya ce Tinubu ya yi wannan alkawarin ne yayin da gwamnoni suka kai masa ziyarar gaisuwar sallar a Abuja.

Bukatar Tinubu ga Dauda Lawal na Zamfara

"Yayin da suke tattaunawa da Dauda Lawal, Tinubu ya tambaye shi halin da ake ciki."
"Gwamna ya fadawa shugaban irin nasarorin da aka samu a kokarin yaki da ta'addanci a Zamfara."
"Tinubu ya yi masa alkawarin karin jami'an tsaro inda ya ce ya himmatu wurin tabbatar da kawo karshen matsalar."
"Tinubu ya bukaci gwamnan ya rinka ba shi bayanai a kai-a-kai domin kawo karshen matsalar a jihar."

Kara karanta wannan

Ana cikin jimamin mutuwar jarumar fina-finai, Gwamna ya bukaci tono gawarta daga kabari

- Suleiman Bala Idris

Minista ya nemi hadin kan 'yan Najeriya

Kun ji cewa ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bukaci hadin kan 'yan Najeriya ga Shugaba Bola Tinubu domin inganta ƙasar.

Idris ya ce Tinubu ya kawo tsare-tsare domin inganta 'yan Najeriya inda ya ce babban abin da ya ke bukata shi ne hadin kai.

Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke cikin wani irin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki da tsadar kayayyaki musamman bangaren abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel