Sarakuna 20 a Arewa Sun Nemi Taimakon Dakarun Igboho kan Hare Haren Ƴan Ta'adda
- Kimanin sarakunan gargajiya 20 da suka tsere daga garuruwansu saboda hare-haren 'yan bindiga sun fara neman mafita
- An tabbatar da cewa sarakunan sun nemi taimakon rundunar tsaro ta Iru Ekun karkashin dan gwagwarmaya, Sunday Igboho
- An ce jami'an Iru Ekun sun isa Isanlu Isin da kewaye domin tantance yanayin tsaro, yayin da sarakuna da mazauna yankunan suka yi fatan zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Kimanin sarakunan gargajiya 20 daga garuruwan da hare-haren 'yan bindiga suka shafa sun koka kan rashin tsaro.
Sarakunan daga jihar Kwara sun nemi taimakon rundunar tsaro mai zaman kanta ta Iru Ekun, wadda ke karkashin jagorancin mai fafutukar Yarabawa, Sunday Igboho.

Source: Facebook
Hare-hare ya daidaita Kudancin Kwara
An ce matakin ya biyo bayan yadda hare-haren 'yan bindiga suka tilasta wa mazauna da sarakunan gargajiya na garuruwa da kauyuka da dama, musamman a Kwara ta Kudu, barin gidajensu, cewar The Nation.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa masu koyon karatun Alkur'ani wuta a Bauchi
Tun daga lokacin, sarakunan gargajiya da wasu mazauna yankunan da abin ya shafa sun koma Ilorin da sauran al'ummomin da ke kusa da babban birnin domin samun kariya.
Rahotanni sun bayyana cewa, ko da yake Sunday Igboho bai kai ziyara da kansa zuwa Kwara ta Kudu ba, jami'ansa sun riga sun isa yankin.
An ce jami'an sun fara aiki musamman a garin Isanlu Isin da sauran al'ummomin da ke makwabtaka da shi domin nazarin yanayin tsaro da tsara hanyoyin tinkarar matsalolin yankin.

Source: Original
Bayanin basarake game da matakin da suka dauka
Da yake tabbatar da hakan ga manema labarai a Ilorin, Sarkin Owa Onire, Oba AbdulRahman Fabiyi, wanda ya koma Ilorin saboda matsalar tsaro, ya ce yana sane da zuwan mutanen Sunday Igboho.
Ya ce:
"Eh, na san mutanen Sunday Igboho suna Kwara ta Kudu, amma har yanzu ba su isa al'ummata ta Owa-Onire ba. Na je garina kwanaki shida da suka gabata, kuma ina ci gaba da tuntubar jama'ata."
Sarkin ya kara da cewa wannan ci gaba abin maraba ne, yana mai addu'ar kokarin da ake yi ya samar da sakamako domin su samu damar komawa garuruwansu cikin kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan
DSS da yan sanda sun yi bincike, an ji gaskiya kan ɓullar sabuwar ƙungiyar ta'addanci a Najeriya
Shi ma Mai Kula da Joint Security Watch a Kwara ta Kudu, Olaitan Oyin-Zubair, ya tabbatar da batun, yana cewa sojoji da tawagarsa sun gudanar da taron tsaro tare da jami'an Iru Ekun.
Sai dai ya bukaci tawagar karkashin jagorancin Muyiwa Adeniyi ta ba da fifiko wajen ceto mutanen da ke hannun 'yan ta'adda da kuma tabbatar da dawowar mazauna garuruwan da aka tilasta wa gudun hijira, cewar Vanguard.
Yan bindiga sun gwabza da yaran Igboho
Mun ba ku labarin cewa rahotanni da suka fito daga Oyo sun nuna cewa an jikkata wasu jami'an sa-kai da ke da alaka da Sunday Igboho da suka je fafatawa da 'yan bindiga.
Tawagar tsaron Iru Ekun da ke da alaka da Igboho na gudanar da sintiri a daji ne domin gano maboyar masu garkuwa da mutane da sauransu.
Duk da yadda labarin ya bazu, zuwa yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka ji rauni ba kuma 'yan sandan jihar Oyo ba su fitar da sanarwa ba.
Asali: Legit.ng