An Sake Kai Harin da Ya Yi Sanadiyyar Kashe Mutane 10 a Jihar Plateau, Jama’a Sun Shiga Firgici

An Sake Kai Harin da Ya Yi Sanadiyyar Kashe Mutane 10 a Jihar Plateau, Jama’a Sun Shiga Firgici

  • Wasu 'yan bindiga sun kai hari tare da kashe mutane da yawa a jihar Plateau, lamarin da ya tada hankalin jama'a
  • Majiya ta bayyana yadda harin ya kai ga kashe mutana biyar 'yan dangi daya da basu ji basu gani ba a yankin
  • Jihar Plateau na daga jihohin Najeriya da ke yawan samun hare-hare da tashe-tashen hankula na tsawon lokaci

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Plateau - Akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai kauyukan Mandung-Mushu da Kopnanle na karamar hukumar Bokkos ta jihar Plateau.

Rahoton da muka samo ya ce, an fara kai harin ne da misalin karfe 10 na daren Juma’a bayan mutanen kauyen suka gama harkokinsu na rana suka shiga bacci da dare.

Kara karanta wannan

Akwai dalili: Shekara 1 na Shugaba Tinubu ta fi shekaru 8 na mulkin Manjo Buhari, Reno Omokri

Wata majiya ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa, harin ya haifar da tashin hankali a cikin garin na Bokkos da kewaye.

An kashe wadanda basu ji basu gani ba a Plateau
'Yan ta'adda sun kashe jama'a a Plateau | Hoto: Nigeria Police Force, Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba

Hakazalika, majiyar ta ce, tuni wadanda harin ya rutsa da su da kuma wadanda suka samu raunuka aka gaggauta kai su asibitin da ke garin.

Majiyar ta ce an kashe mutum biyar daga iyali daya a harin, inda aka gano cewa, a hari irin wannan aka kashe wata mata mai juna biyu 'yar dangin a makon jiya.

A cikin wata sanarwa da kungiyar Bokkos Cultural Development Council (BCDC) ta fitar, ta yi Allah-wadai da harin da ya kai ga mutuwar talikan mazauna yankin.

Jami'an tsaro na kusa, amma aka kashe jama'a

Kungiyar ta ce maharan sun kai harin ne kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, wadanda ba sa dauke makami a lokacin da suke hutawa da dare.

Kara karanta wannan

Fusatattun Yarbawa na son a raba Najeriya, sun farmaki sakateriyar gwamnati a Oyo

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban BCDC Vanguard, Barr. Farmasum Fuddang, ta ce abin takaicin ya faru ne duk da kasancewar jami’an tsaro a kusa da yankin, kamar yadda Daily Trust din ta tattaro.

Ba wannan ne karon farko da ake kai hare-hare a yankunan jihar Plateau ba, hakan ya zama ruwan dare a cikin 'yan shekarun nan.

Fulani na zargin sojoji da yi masu barna a Plateau

A wani labarin, kun ji yadda Fulani mazauna Plateau suka bayyana kukansu kan yadda ake barnata dukiyarsu a jihar.

Sun koka da cewa, an kai masu hari alhalin basu aikata komai ba, lamarin da ya jawo masu asarar dukiya mai yawa.

Ana yawan samun sabani tsakanin manoma da makiyaya a jihar ta Plateau, har yanzu ba a warware matsalar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel