Gwamnan Katsina Ya Rabawa Jami'an Tsaro Motocin Kawo Karshen 'Yan Bindiga

Gwamnan Katsina Ya Rabawa Jami'an Tsaro Motocin Kawo Karshen 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin jihar Katsina ta rarraba motoci masu sulke guda goma ga jami'an tsaron jihar domin taimaka musu wajen magance rashin tsaro
  • Yankunan da rashin taron ya yi kamari, irinsu Jibiya, Safana, Danmusa da Kankara na daga yankunan da motocin za su yi aiki gadan-gadan
  • Rashin tsaron da ya addabi jihar Katsina na daga abubuwan da gwamna Radda ya sha yin magana a kai, har ya ke cewa zai iya sadaukar da rayuwarsa don tabbatar da tsaro

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina -Gwamnatin jihar Katsina ta rarraba motocin yaki guda goma ga jami'an tsaro domin taimaka musu wajen dakile rashin tsaro.

Kara karanta wannan

"Akwai damuwa" Gwamna Sule ya jero ƙananan hukumomi 8 da ke cikin babbar matsala

Gwamnan jihar, Dikko Ummaru Radda ne ya rarraba motocin a ranar Litinin, kuma ya bayar da su ne ga yankunan da rashin tsaro ya yi kamari.

Yankunan da suka samu motocin sun hada da Jibiya da Safana da Danmusa da Kankara da Batsari da Faskari da Ɗandume da kuma Sabuwa.

Gwamna Umaru Dikko
Gwamnatin Katsina ta Raba Motoci Masu Sulke ga Jami'an Tsaro Hoto:@KatsinaStateN
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihar Katsina a baya-bayan nan ta shiga jerin jihohin Arewa dake fama da matsalar yan bindiga da sauran matsalolin tsaro, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A karin bayanin da ya yiwa BBC hausa, Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kastina, Nasiru Mu'azu ya ce motoci ne masu sulke a raba ga jami’an tsaron.

"Mun gaji rashin tsaro," Gwamnan Katsina

Gwamna Radda, ta bakin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida ya tabbatar da daga matsalolin da suka gada a jihar Katsina akwai rashin tsaro da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Iftila'i: Mummunar gobara ta shafe kasuwar Boda dake Gaya

Yana fatan motocin masu sulke da suka raba za su taimaka wajen fatattakar masu garkuwa da mutane da suka addabi wasu yankunan jihar, kamar yadda Leadership News ta wallafa.

Gwamnan ya yiwa jama'ar jihar alkawarin gwamnati na tare da su, kuma ana ci gaba da dubo hanyoyin tabbatar da tsaro a jihar.

Gwamnati ta sha alwashin magance rashin tsaro

A baya kun ji yadda Gwamna Umaru Dikko Radda ya ce zai duk abinda ya kamata domin kakkabe rashin tsaro daga birnin Katsina da kewaye.

Gwamnan ya ce a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa domin ganin an samu wanzuwar zaman lafiya tsakanin al’umar da suka zabe shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel