Sojoji Sun Cafke Mutum 6 Masu Yi Wa 'Yan Ta'adda Safarar Kayayyaki a Borno

Sojoji Sun Cafke Mutum 6 Masu Yi Wa 'Yan Ta'adda Safarar Kayayyaki a Borno

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke miyagu masu yi wa ƴan ta'addan Boko Haram safarar kayayyaki Borno
  • Sojojin sun cafke mutanen su shida ɗauke da kayayyakin da kuɗaɗensu sun kai N2m a safiyar ranar Asaabar, 13 ga watan Afirilun 2024
  • Mutanen dai suna karɓo kayayyaki a wajen ƴan ta'addan domin kai wa kasuwa su sayar sannan su mayarwa da ƴan ta'adda kuɗaɗen

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojoji sun cafke aƙalla mutum shida masu yi wa ƴan ta'addan Boko Haram safarar kayayyaki a jihar Borno.

Sojojin sun cafke ɓata garin ne tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro a ranar Asabar, 13 ga watan Afirilun 2024.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da dama sun mutu a wani sabon fada tsakanin mayakan ISWAP da Boko Haram

Sojoji sun cafke miyagu s Borno
Sojoji sun kama masu yi wa 'yan ta'adda safarar kayayyaki a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Sojojin na Bataliya ta 112 na Operation Hadin Kai sun yi caraf da mutanen ne a ƙaramar hukumar Mafa ta jihar bayan sun fito bakin aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka cafke mutanen

Majiyoyi masu ƙarfi sun shaidawa Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro da yaƙi da ta'addanci a yankin tafkin Chadi yadda aka kama mutanen.

Majiyoyin sun bayyana cewa an cafke mutanen ɗauke da kayayyakin da kuɗaɗensu sun kai N2m a cikin wata mota ƙirar Isuzu.

Majiyoyin sun bayyana cewa:

"Bayanan mutanen da aka sace su ne Usman Gujja, Abu Hamman Dawud, Ramat Ibrahim, Hala Hadum, Alhaji Kawu da Bulama Ali Boscoro (direba)."

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa mutanen na ƙarbo kayayyakin ne da suka haɗa da gawayi daga hannun ƴan ta'addan, su kai kasuwa su sayar sannan su mayar musu da kuɗaɗen.

Kara karanta wannan

DHQ: Dakarun sojoji sun halaka ƴan bindiga sama da 150, sun samu nasarori a Arewacin Najeriya

An dai tsare waɗanda ake zargin a hannun sojoji domin ci gaba da gudanar da bincike.

Sojoji sun kashe ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa ta kashe ƴan ta’adda shida da suka kashe jami’anta a hanyar Biu-Buni-Yadi, a jihar Borno.

Sojojin sun kuma ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda biyar da alburusai a hannun ƴan ta'addan bayan sun yi musayar wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel