Uba Sani Ya Yi Maganar El Rufai, Ya Bayyana Kallon da Yake Masa

Uba Sani Ya Yi Maganar El Rufai, Ya Bayyana Kallon da Yake Masa

  • Uba Sani ya ce bai taba fadin wani abu mara kyau game da Nasir El-Rufai ba, kuma ba zai taba yin hakan ba duk da rashin jituwar da ake zargin tana tsakaninsu
  • Gwamnan ya ce shirunsa kan shari’ar El-Rufai ba yana nufin ya yi watsi da shi ba, yana mai cewa ya dauki matakai na nuna masa girmamawa
  • Uba Sani ya bayyana cewa har yanzu yana tuntubar tsofaffin gwamnoni domin amfana da kwarewarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Kaduna, jihar Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan magabacinsa, Malam Nasir Ahmad El-Rifai.

Gwamna Uba Sani ya ce bai taba fadin wani abu mara kyau game da Nasir El-Rufai ba, duk da rade-radin rashin kyakkyawar alaka da ake ganin ta shiga tsakaninsu.

Uba Sani ya yi maganar El-Rufai
Malam Nasir Ahmad El-Rufai tare da Uba Sani Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Facebook

Uba Sani ya bayyana hakan ne a wata hira da shirin Daily Politics na tashar Trust TV, wanda aka watsa ranar Talata, 27 ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan

Ziyarar Hannatu Musawa ofishin uban ‘ya ‘yanta, Abdussamad ya dawo da batun aure

Gwamnan ya ce har yanzu yana matukar girmama El-Rufai, duk da tsawaita zaman da tsohon gwamnan ya yi a tsare.

“Maganar gaskiya, ba ni da wata matsala da shi. Idan kuka saurare ni da kyau, ban taba fadin wani abu mara kyau game da shi ba, kuma ba zan taba yin hakan ba,” in ji Uba Sani.

El-Rufai na fuskantar shari’a

Tsohon gwamnan na Kaduna na fuskantar shari’a kan zarge-zargen halasta kudaden haram da karkatar da kadarorin gwamnati.

Tun ranar 19 ga Fabrairu, El-Rufai yake tsare a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffuka Masu Alaka da Hakan (ICPC), bayan Hukumar EFCC ta sake shi.

Sai dai Uba Sani ya ce shirunsa kan shari’ar tsohon gwamnan bai kamata a dauke shi a matsayin ya yi watsi da shi ba.

Ya bayyana cewa ya dauki matakai da dama domin nuna girmamawa ga El-Rufai, amma ba ya son bayyana su a bainar jama’a.

Kara karanta wannan

Isa Ashiru ya fito da gaskiyar zance bisa zargin ya fallasa El Rufai kan rashin tsaro a Kaduna

"Mutane ba za su fahimci wasu abubuwa ba. Ni mutum ne mai kiyaye sirri, kuma saboda girmamawa, akwai abubuwa da dama da na yi domin nuna masa matsayinsa a wurina, amma ba na ganin ya dace na fito na bayyana su.” In ji shi.

Ya kara da cewa mutunta mutum na nufin akwai wasu abubuwa da bai kamata a rika bayyanawa jama’a ba.

Ya ce bai janye kalaman yabon El-Rufai ba

Uba Sani ya jaddada cewa bai taba musanta ko janye kalaman alherin da ya taba yi game da El-Rufai ba.

“Zan iya gaya muku a yau cewa duk abin da na taba fada game da shi, ban taba dawowa na karyata shi ba. Kun taba ganina na karyata wani abu da na fada? A’a. Haka halina yake.” In ji shi.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa yana tuntubar tsofaffin gwamnoni domin neman shawarwari kan wasu batutuwan mulki.

Uba Sani na girmama El-Rufai
Gwamna Uba Sani na jawabi a wajen taro Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Isa Ashiru ya musanta maganar El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa Isa Ashiru Kudan ya yi martani kan zargin cewa ya dora alhaki ga Nasir El-Rufai kan tabarbarewar tsaro a jihar.

Isa Ashiru Kudan ya musanta zargin cewa ya ɗora wa tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, alhakin ƙaruwa da taɓarɓarewar matsalar tsaro a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng