Juyin-Mulki: Ministan Waje Ya Yi Maganar Yiwuwar Hambarar da Mulki a Najeriya

Juyin-Mulki: Ministan Waje Ya Yi Maganar Yiwuwar Hambarar da Mulki a Najeriya

  • Ministan harkokin wajen Najeriya ya ce a zamanin nan, da kamar wuya Sojoji su iya kifar da gwamnati
  • Geoffrey Onyeama bai ganin yiwuwar a hambarar da gwamanti yadda ake yi a wasu kasashen Afrika
  • Ministan ya ke cewa mulkin farar hula ya yi karfi a Najeriya, an yi shekaru 24 a tsarin damukaradiyya

Abuja - Daga 1960 da Najeriya ta samu ‘yancin kai zuwa yanzu, an yi juyin mulki iri-iri, amma Geoffrey Onyeama ya na ganin zamanin hakan ya wuce.

A wata zantawa ta musamman da Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ya yi da Premium Times, ya ce da wahala a hambarar da gwamnati a yau.

Onyeama ya ce yana da matukar wahala sojoji su iya yin juyin mulki a halin yanzu a Najeriya.

Sojoji
Shugaban kasa tare da manyan Sojoji Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Ministan harkokin kasar wajen ya ce tun da aka yi shekaru 24 ana canza gwamnatocin farar hula, an fi karfin sojoji su yi karambanin karbar mulki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Fitaccen Malami a Arewacin Najeriya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Juyin mulki a Afrika

Daga 2020 zuwa yanzu, an kifar da gwamnatoci biyar a Afrika ta yamma - Burkina Faso, Mali da Guinea, an nemi yin haka a Gambia da Guinea-Bissau.

A kasar Chadi da ke makwabtaka da Najeriya an samu canjin gwamnati a 2021 inda Laftana Janar Mahamat Idriss Déby ya jagoranci hambarar da mulki.

Ana fuskantar barazana daga masu fafutukar a raba kasa a Kudancin Najeriya, amma Ministan ya ce gwamnati ba za ta bari abin ya tabarbare ba.

Kamar yadda Onyeama ya shaidawa jaridar, gwamnatin tarayya ba za ta bari abubuwa su fi karfin hukuma ba, za ayi maganin masu tada kayar baya.

Duk barazanar da aka fuskanta, Ministan ya ce an iya shawo kan su, saboda haka yake ganin za a iya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Dubu ta Cika: Sojoji Sun Kwamushe Rikakken Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanan Sirri a Arewa

Za a shiga matsala

Cheta Nwanze wanda masani ne a kan harkar tsaro, ya ce idan sojoji su ka yi juyin mulki a Najeriya, hakan zai jefa sauran kasashen Afrika a matsala.

A cewar Nwanze, hakan zai jawo gwamnatocin farar hula da ke nahiyar su shiga barazana.

Kujerar karamin Minista

Majalisar zartarwa ta kasa watau FEC tayi zaman da ya kasance na ban-kwana a ranar Laraba. A nan ne aka ji labari Ministoci sun yi jawabin sallama.

Ministoci irinsu Festus Keyamo da Ramatu Tijjani Aliyu sun fito karara su ka fadawa Shugaban kasa abin da suke ganin shi ne daidai wajen nada Minista.

Asali: Legit.ng

Online view pixel