Gwamnatin Tinubu Ta Ɗauko Hanyar Gyara, Za a Samu Rangwame na Kwana 90
- Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa ta amince da shirin kwanaki 90 domin rage tsadar rayuwa, sauƙaƙa farashin abinci
- Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci gwamnonin jihohi tabbatar da cewa sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu sun inganta rayuwar 'yan Najeriya
- Majalisar ta kuma amince da haɗin gwiwar gwamnati wajen rage kuɗin sufuri, yaƙi da cutar Ebola, kawar da cutar shan inna da bunƙasa kiwon dabbobi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa ta amince da wani shirin tattalin arziki na kwanaki 90 domin rage tsadar rayuwa, sauƙaƙa farashin abinci da jawo masu zuba jari a Najeriya.
Ma'aikatar Kuɗi ta Tarayya ce ta gabatar da shirin, wanda majalisar ta amince da shi ranar Alhamis yayin taronta na 161, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranta ta yanar gizo.

Source: UGC
A cewar sanarwar da Stanley Nkwocha, Babban Mataimaki na Musamman ga Shettima kan Yaɗa Labarai da Sadarwa, ya fitar a shafinsa a X.
Waɗannan fannoni sun haɗa da sauƙaƙa farashin abinci, daidaita haraji, kammala manyan ayyukan raya ƙasa, warware matsalolin da ke hana zuba jari da kuma bayar da tallafi ga gidaje bisa ƙa'ida.
Majalisar ta kuma amince da kafa wani dandali na ƙasa domin bibiyar ayyukan raya ƙasa a sassan Najeriya, tare da mai da hankali kan gaskiya, riƙon amana da bayyana yadda ake amfani da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin man fetur.
Da yake jawabi yayin taron, Shettima ya buƙaci gwamnonin jihohi da hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki su tabbatar da cewa alfanun sauye-sauyen tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu sun inganta rayuwar 'yan Najeriya.
Ya ce ya kamata a auna nasarar manufofin tattalin arziki ta hanyar tasirinsu ga rayuwar yau da kullum, ciki har da samun sufuri mai araha, kiwon lafiya, guraben ayyukan yi da tsaro na kuɗi.

Kara karanta wannan
Dan majalisa ya hango matsala a dokar zabe da za ta iya shafar sahihancin zaben 2027
Shettima ya ce:
“Amfanin farko na wadata shi ne mutum ya samu kwarin gwiwar tsara rayuwarsa. Aikinmu shi ne tabbatar da cewa wannan kwarin gwiwa ba ya dogara sosai da sa'a.”
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi, yana mai cewa bambancin nauyin da ke kansu bai kamata ya hana samar da muhimman ayyuka ba.
Ya ce:
“Nauyin da aka ɗora wa kowannenmu bai kamata ya zama uzurin gasa tsakaninmu ba. Kowane gwamna yana da masaniyar da babu wata takardar gwamnatin tarayya da za ta iya bayarwa.”
Rage kuɗin sufuri ga yan kasa
Dangane da sufuri, Shettima ya ce ya kamata a auna nasarar Shirin Motocin Iskar Gas ta Ƙasa (CNG) bisa yadda yake rage kuɗin da fasinjoji ke kashewa, ba yawan motocin da aka samar ba.
Ya ce:
“Kuɗin zuwa wurin neman abin rayuwa bai kamata ya cinye abin da mutum zai samu ba. Ya kamata a duba nasara ta fuskar arahar sufuri da sauƙin samunsa, ba yawan motocin da aka girka ba.”
Majalisar ta kuma amince da kafa tsarin samar da kuɗaɗen haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi domin hanzarta amfani da motocin CNG da motocin lantarki.
Ta umarci hukumomin da abin ya shafa su tattauna da ƙungiyoyin ma'aikatan sufuri da masu gudanar da harkokin sufuri domin tabbatar da cewa an mayar da ribar da aka samu daga amfani da motocin ga fasinjoji ta hanyar rage kuɗin mota.
Ƙarin bayani na tafe ....
Asali: Legit.ng

