Fadar Gumel Ta Kawo Dokar Daukar Hoto da Bidiyo bayan Abin da Ya Faru a Daura
- Majalisar Masarautar Gumel da ke jihar Jigawa ta haramta ɗaukar hotuna da bidiyo tare da yaɗa bayanai game da masarautar ba tare da samun izininta ba
- Masarautar ta ce matakin na da nufin daidaita yadda ake yaɗa bayanai da kuma kare muhimman bayananta daga fitarwa ba bisa ƙa'ida ba
- Rahotanni sun bayyana cewa ta kuma gargaɗi duk wanda ya karya dokar cewa zai fuskanci matakin shari’a da ya dace da laifin da ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa – Majalisar Masarautar Gumel da ke jihar Jigawa ta haramta ɗaukar hotuna da bidiyo a masarautar, tare da yaɗa bayanai game da ita ba tare da izinin fadar masarautar ba.
Sakataren majalisar masarautar, Murtala Aliyu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Laraba.

Kara karanta wannan
Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa ya ce an ɗauki matakin ne domin tsara yadda ake sadarwa da jama’a da kuma kare bayanan masarautar daga yaɗawa ba tare da izini ba.
Masarauta ta hana ɗaukar hoto
Aliyu ya bayyana cewa mutanen da fadar masarautar ba ta amince da su a matsayin jami’an yaɗa labarai ba su da ikon ɗaukar hotuna, yin bidiyo ko tattara bayanai a madadin masarautar ba tare da izini ba.
Rahotanni sun nuna cewa ya ce wannan doka ta shafi duk wani aiki da ya shafi tattara bayanai ko yaɗa su da sunan masarautar.
An hana amfani da sunan masarautar
Sanarwar ta kuma bayyana cewa an haramta amfani da sunan masarautar wajen wallafa sanarwa ko rahotanni ba tare da izinin fadar ba.
Haka kuma, majalisar ta hana ƙirƙirar shafukan sada zumunta da ke ɗauke da sunayen da suka danganci masarautar ba tare da amincewarta ba.
Sakataren fadar Sarkin Gumel ya ce duk wanda ya karya waɗannan dokoki zai fuskanci matakin shari’a da ya dace.

Source: Facebook
Bayanan da ta yarda a yaɗa
Aliyu ya ce bayanan da aka tabbatar sun fito daga majiyoyin da fadar masarautar ta amince da su ne kaɗai za a iya sake yaɗawa.
Ya bayyana cewa matakan na da nufin tabbatar da cewa bayanan da ake fitarwa ga jama’a game da masarautar sahihai ne kuma an amince da su.
Ya ƙara da cewa masarautar za ta ci gaba da bin tsarin sadarwa mai kyau tare da kare martabarta da bayananta na hukuma.
Radda ya ziyarci fadar Daura
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya ce kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Shugaba Bola Tinubu da marigayi Muhammadu Buhari ta ƙarfafa zumuncin Fadar Shugaban Ƙasa da al’ummar Daura.
Radda ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai gidan Sardaunan Daura, Alhaji Auwalu Umar Faruq, tare da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu–Dikko–Jobe.
Gwamnan ya kuma nemi addu’a da goyon bayan sarakunan gargajiya da al’ummar Daura ga ’yan takarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027 da ke tafe.
Asali: Legit.ng
