Wike Ya Maida wa Amaechi Martani da Ya Ji Ana Lissafin Wuraren da Atiku Zai Ci Zabe

Wike Ya Maida wa Amaechi Martani da Ya Ji Ana Lissafin Wuraren da Atiku Zai Ci Zabe

  • Nyesom Wike ya bukaci masu tallar Bola Tinubu su hana ADC da NDC samun 25% na kuri'un Abuja a zaben 2027
  • Ministan ya bukaci ‘yan kwamitin yakin neman zaben APC su kara kaimi wajen karya musamman ADC da NDC
  • Wike Ya ce ayyukan Bola Tinubu a Abuja za su taimaka wajen jawo wa APC kuri'u, akasin hasashen wasu ‘yan adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Nyesom Wike wanda shi ne Babban Ministan harkokin birnin tarayya Abuja ya umarci ‘yan kwamitin yakin zaben Bola Tinubu su dage da kamfe.

Ministan na Abuja ya umarci kwamitin kamfen Bola Tinubu su hana jam’iyyun adawa samun ko da 25% na kuri’un da jama’a za su kada a zaben 2027.

Nyesom Wike
Nyesom Wike tare da Bola Tinubu a wajen kamfen APC Hoto: @LereOlayinka
Source: Twitter

Nyesom Wike ya kaddamar da kwamitin zaben APC

Daga The Cable aka fahimci ya yi wannan magana ne lokacin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben da kuma kungiyar Rainbow Coalition a Abuja.

Kara karanta wannan

"Alamu da lissafin siyasa sun nuna wanda zai lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027"

Nyesom Wike ya kaddamar da kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC mai mutane 466.

A wani jawabi da Lere Olayinka ya fitar, Nyesom Wike ya ce ya zama dole ‘yan kwamitin su dage wajen ganin sun hana ADC da NDC samun ko da 25%.

An bukaci 'yan kamfe su ba Bola Tinubu nasara

Tsohon gwamnan na Rivers ya fada masu cewa aikinsu shi ne ganin Bola Tinubu da ‘yan takaran APC a zaben Majalisar tarayya sun samu babbar nasara.

Nyesom Wike ya fada masu:

“Ba wai muna magana ne kan yin nasara kawai ba; muna magana ne kan samun gagarumar nasara,”
“Dole ne mu hana su samun kashi 25% na kuri’un. Ba su cancanci samun wannan kaso ba.”

Wike bai so farin jinin Atiku ya shigo Abuja

Wike ya yi watsi da ‘yan adawa musamman na ADC da suke tunkaho da farin jinin Atiku Abubakar a 2027, suna hangen nasararsa a jihohi Arewa 13.

Kara karanta wannan

Tinubu ya leƙo babbar matsalar ƴan Plateau, ya ɗauka masu alƙawari

‘Dan siyasar ya dage cewa babu yadda Atiku Abubakar zai yi da kuri’un mutanen birnin Abuja.

A jawabin da ya yi a wajen, an ce ya caccaki Atiku, yana mai cewa babu wan cigaban da ya kawo wa Abuja lokacin da ya ke mataikakin shugaban kasa.

Ministan Abuja ya bi ta kan Rotimi Amaechi

Haka zalika ya dura kan Rotimi Amaechi, yana mai kalubalantar shi ya jarraba karbuwarsa a Rivers, yana mai hangen nasara a mahaifarsa da Abuja.

A wani bidiyo da Emma Ikumeh ya daura a X, an ji Wike yana fada wa Amaechi cewa maganar a ce Atiku yana da jihohin Arewa 13 sam ba haka ba ne.

Daga raddin da ya yi wa Rotimi Amaechi aka ji yadda yake alwashin samun nasarar APC a Birnin tarayya.

“Abuja ba ta kowace jam’iyya ba ce illa APC.”

Jagoran na PDP ya yi bayanin irin ayyukan da gwamnatin Bola Tinubu ta yi a Abuja daga ciki har da tituna da kuma shirin kafa jam’iyyar kimiyya a Abaji.

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya yi magana kan damar Atiku da Obi a 2027

Da irin wadannan ayyuka da mutane suke gani, Wike yake sa ran shugaba Tinubu zai yi nasara.

Abin da Atiku Abubakar ya fada a Bauchi

Rahoto ya zo cewa Atiku Abubakar ya sha alwashin ci gaba da aikin hako mai a rijiyar Kolmani idan aka zabi ADC ta hau mulki a shekara mai zuwa.

'Dan takaran shugaban kasar na ADC ya kuma yi alkawarin dawo da tallafin man fetur da na wutar lantarki tare da magance matsalar tsaro a Najeriya.

Atiku Abubakar ya bukaci al'ummar Bauchi su zabi ADC a 2027 tare da kare kuri'unsu don hana magudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng