2027: Gwamna Ya Ce Nasarorin da Ya Samu Za Su Taimaka Masa wajen Zama Shugaban Kasa
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APM kuma gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce nasarorin da ya samu za su taimaka masa a 2027
- Gwamnan Oyo ya ce ƙarin mafi ƙarancin albashi da biyan ma’aikata albashi a kan lokaci na daga cikin nasarorin gwamnatinsa a Oyo
- Makinde ya ce gwamnatinsa ta zuba jari a noma da gine-ginen ababen more rayuwa domin bunƙasa tattalin arzikin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - Gwamna Seyi Makinde, ya ce ayyukan da ya gudanar a jihar Oyo na kimanin shekaru takwas sun ba shi kwarin gwiwar fuskantar zaɓen 2027.
Ya bayyana ƙarin mafi ƙarancin albashi, biyan ma’aikata albashi a kan lokaci, zuba jari a fannin noma da ababen more rayuwa, da tallafa wa fitar da amfanin gona zuwa kasuwannin duniya a matsayin wasu daga cikin nasarorin gwamnatinsa.

Kara karanta wannan
"Alaƙa tsakanin Tinubu da gwamna ta yi tsami saboda neman takarar shugaban ƙasa a 2027"

Source: Facebook
Makinde, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise Television a ranar Juma’a.
Gwamna ya yi nazarin halin da ake ciki
Ya kwatanta salon tafiyar da gwamnatinsa da manufofin tattalin arzikin gwamnatin tarayya, inda ya ce ya kamata a auna nasarar sauye-sauyen tattalin arziki bisa tasirinsu ga rayuwar al’umma.
Gwamnan ya kuma ce bunƙasar tattalin arziki da yawan ajiyar kuɗaɗen ƙasa ba su da wani amfani sosai idan har ’yan Najeriya na fama da yunwa, sannan iyalai ba sa iya biyan buƙatunsu na yau da kullum.
“Ɗaukar ƙananan matakan gyara nan da can ba zai yi aiki ba, idan ana cewa abubuwa na faruwa a matakin tattalin arziki gaba ɗaya, sannan tasirinsu zai sauka zuwa matakin rayuwar jama’a, a ganina waɗannan uzuri ne kawai.
"Ana ta bayanin cewa muna da tarin kuɗaɗe a ajiye. Mene ne tasirin hakan ga talakan da ke kan titi? Shin ’yan Najeriya na fama da yunwa? Shin iyalai da dama na iya sayen wasu abubuwa?” in ji Makinde.
Makinde ya fadi nasarorinsa a Oyo
Makinde ya kawo misalin mafi ƙarancin albashin ma’aikata a Jihar Oyo a lokacin mulkinsa, inda ya ce an fara da N18,000, aka mayar da shi N30,000, sannan daga baya aka ƙara shi zuwa tsakanin N70,000 da N80,000.
“Game da albashi fa? Lokacin da na hau mulki, na tarar da mafi ƙarancin albashi na N18,000, muka ƙara shi zuwa N30,000 cikin shekaru sama da bakwai.
"Lokacin da wannan gwamnatin tarayya ta fara aiki a 2023, abubuwa sun rikice sosai, sai muka sake ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N70,000, N75,000 da N80,000,” in ji shi.

Source: Facebook
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ba ta taɓa jinkirta biyan albashin ma’aikata ba a tsawon lokacin da ya yi yana mulki, har ma a lokacin gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.
Makinde ya jero dalilin gwabzawa da Tinubu
Kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana dalilan da suka sa yanzu zai kalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 duk da ya goyi bayansa a 2023.
Makinde, ya ce matakin da ya dauka ba ya da nasaba da wata rashin jituwa ta kashin kai tsakaninsa da Tinubu ko kuma burinsa na zama shugaban kasa, sai dai damuwa ce kan makomar Najeriya.
Asali: Legit.ng
