Tashin Hankali: Yan Ta'adda Sun Kai Hari kan Tawagar Sanata Monguno da Wasu Jiga-Jigan APC

Tashin Hankali: Yan Ta'adda Sun Kai Hari kan Tawagar Sanata Monguno da Wasu Jiga-Jigan APC

  • Sanata Mohammed Tahir Monguno da wasu jiga-jigan APC sun tsallake wani yunƙurin harin Boko Haram a ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno
  • Rahotanni sun ce ’yan ta’addan sun harba makamai guda uku zuwa garin a lokacin da ’yan siyasar ke gudanar da yaƙin neman zaɓen 2027
  • Dakarun Operation Hadin Kai sun dakile harin, inda tawagar ’yan siyasar ta koma Monguno cikin aminci ba tare da asarar rai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - Babban mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa, kuma sanatan da ke wakiltar Borno ta Arewa, Mohammed Tahir Monguno, tare da wasu jiga-jigan APC sun tsallake wani yunƙurin harin Boko Haram a ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

Majiyoyi sun bayyana cewa Monguno da tsohon gwamnan jihar, wanda kuma sanata ne, Maina Maaji Lawan, da wasu ’yan siyasa, sun isa Kukawa domin ci gaba da rangadin yaƙin neman zaɓensu na 2027.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa

Monguno.
Sanata mai wakiltar Borno ta Arewa, Mohammed Tahir Monguno Hoto: Mohammed Tahir Monguno
Source: Facebook

Monguno ya halarci kamfe da Zulum

Vanguard ta ruwaito cewa tun da farko, Monguno ya halarci ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen a hukumance tare da Gwamna Babagana Zulum a garin Monguno ranar Lahadin da ta gabata.

Sai dai gwamnan ya bar Monguno zuwa Maiduguri a ranar Litinin ta jirgin sama mai saukar ungulu, yayin da wasu daga cikin tawagarsa suka isa Maiduguri a wannan rana ta mota.

Majiyoyi sun ce wasu ’yan siyasa, ciki har da babban mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa, sun wuce daga Monguno zuwa Kukawa domin neman goyon bayan masu zaɓe, inda ’yan ta’addan suka yi ƙoƙarin kai hari tare da tarwatsa al’ummar garin.

Yan ta'adda sun yu yunkurin kai hari

An kuma tattaro cewa bisa bayanan sirri da aka samu, dakarun Operation Hadin Kai sun gaggauta ɗaukar mataki tare da dakile yunƙurin harin da ’yan ta’addan suka yi kan tawagar yaƙin neman zaɓen.

Kara karanta wannan

Yadda mai babur ya jawo hatsarin mota, ya rutsa da shugaban APC, daraktan kamfen

A cewar rahoton, ’yan ta’addan sun harba bama-bamai guda uku zuwa Kukawa ranar Litinin, a lokacin da Monguno, tsohon gwamnan jihar Borno Maina Maaji Lawan da wasu ’yan siyasa ke garin domin gudanar da ayyukan yaƙin neman zaɓe.

Rahoton ya ce majiyoyin yankin sun bayyana cewa tun da farko ’yan ta’addan sun yi barazanar kawo cikas ga yaƙin neman zaɓen, lamarin da ya sa aka ƙara tsaurara matakan tsaro.

Sojoji sun dakile shirin 'yan ta'addan

Ya ƙara da cewa dakarun Operation Hadin Kai sun gano motsin ’yan ta’addan a kusa da Kukawa, sannan suka gaggauta mayar da martani tare da hana su kai harin.

Bayan haka, tawagar yaƙin neman zaɓen ta koma Monguno cikin aminci ba tare da wani rauni ko asarar rai ba.

Rahoton ya kuma bayyana cewa ’yan ta’addan sun sake yunƙurin kai hari garin a lokuta daban-daban cikin daren, amma dakarun tsaro sun hana su samun damar shiga garin.

Kun ji cewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262