Sojoji Sun Tabbatar da Bidiyon Gawarsu da 'Yan Bindiga, Sun Fadi Dalili
- Rundunar sojojin Najeriya ta kare ganawar da jami’anta suka yi da ’yan bindiga a jihar Kwara, inda ta ce ba sulhu ko haɗin kai da ’yan ta’adda suka yi ba
- Sojojin sun bayyana cewa ganawar ta taimaka wajen kwato bindigogin AK-47 guda 12 da kuma kuɓutar da mutane 10 da aka yi garkuwa da su
- Rundunar ta ce ’yan bindigar sun nuna shirinsu na miƙa makamansu da sakin mutanen da suke riƙe da su bayan matsin lambar hare-haren sojoji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kwara – Rundunar sojojin Najeriya ta yi karin haske kan bidiyon da ya yaɗu a kafafen sada zumunta na jami’an tsaro suna ganawa da ’yan bindiga a jihar Kwara.
Dakarun Najeriya sun ce ganawar wani ɓangare ne na shirin kwato makamai da kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.

Source: Facebook
Sojoji sun wallafa a Facebook cewa rundunar haɗin gwiwa mai suna Operation Savannah Shield ta ce ba daidai ba ne a fassara ganawar a matsayin alaƙa ko sassauci ga ’yan ta’adda.
Yadda ganawar ta gudana
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa jami’an sojoji da na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ne suka shiga tattaunawar da ’yan bindigar.
Sanarwar da Laftanar Kanal Ibrahim Shittu ya sanya wa hannu ta ce ’yan bindigar sun nuna niyyar miƙa makamansu tare da sakin mutanen da suke garkuwa da su.
Shittu ya bayyana cewa hakan ya biyo bayan hare-haren da sojoji suka ci gaba da kai musu, wanda ya jefa ’yan bindigar cikin matsin lamba, har suka rage musu zaɓi tsakanin miƙa wuya ko fuskantar farmakin sojoji.
An kwato bindigogi 12
A bayanin da aka mika wa manema labarai, rundunar ta ce ganawar ta haifar da nasarar kwato bindigogin AK-47 guda 12 daga hannun ’yan bindigar.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta gano dabarun 'yan kasuwa, za a kawo karshen kauce wa biyan haraji
Haka kuma, Punch ta wallafa cewa an samu nasarar kuɓutar da mutane 10 da aka yi garkuwa da su sakamakon matakin da sojojin suka dauka.

Source: Facebook
Ta bayyana cewa wannan nasara ta nuna tasirin dabarar da rundunar ke amfani da ita ta hanyar tattaunawa da sauran matakan da ba na yaƙi ba, tare da ci gaba da kai hare-haren soji kan ’yan ta’adda da ’yan bindiga.
Ga bidiyon ganawar sojoji da 'yan bindigan a kasa:
An kama mai safarar makami
A wani labarin, mun rahoto cewa dakarun Sojojin Najeriya sun kama wani mutum da ake zargin dillalin harsasai ne, bayan sun gano harsasai da ya ɓoye a cikin buhun wake a jihar Kogi.
An kama wanda ake zargin mai suna Umaru Muhammad, mai shekaru 47, da misalin ƙarfe 9:30 na dare ranar Talata, 17 ga Nuwamba, 2026.
Binciken farko ya nuna cewa ana zargin an shirya kai harsasan ga wasu mutane biyu da aka bayyana da sunayen Gimba da Dare, waɗanda ake cewa mazauna ƙauyen Gori a Kogi.
Asali: Legit.ng
