Shugaba Tinubu Ya Amince da Gina Tashar Jigilar Kaya ta Tsandauri a Jihar Kebbi
- Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa tashar jiragen kaya ta tsandauri a jihar Kebbi domin bunƙasa harkokin kasuwanci da tattalin arziƙi
- Bola Tinubu ya sanar da amincewar ne yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a Birnin Kebbi ranar Talata
- Har yanzu ba a bayyana wurin da za a gina tashar ba, lokacin fara aikin, kuɗin da za a kashe ko lokacin fara gini
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Birnin Kebbi, Nigeria - Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa tashar jiragen kaya ta tsandauri a jihar Kebbi, yana mai cewa aikin ya zama dole domin bunƙasa harkokin tattalin arziƙi a jihar.
Tinubu ya sanar da amincewar ne yau Talata, 17 ga watan Nuwamba, 2026 yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Birnin Kebbi, inda ya yi jawabi ga magoya bayansa da masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan
2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta rahoto cewa bayanai sun nuna cewa Tinubu ya amince da gina tashar, wacce ake ganin za ta bunkasa harkokin kasuwanci da inganta fannin samun kudin shiga a jihar Kebbi.
Tinubu zai gina tashar tsandauri
Da yake jawabi a wurin gangamin kamfen APC, Shugaba Tinubu ya ce:
“Na fahimci buƙatarku ta samun tashar jigilaf kaya ta cikin kass. An amince da ita. Kebbi na buƙatar hakan, kuma na amince."
Amincewar ta biyo bayan buƙatar samar da wannan cibiya, wadda ake sa ran za ta ƙarfafa harkokin kasuwanci da jigilar kaya a jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Tashar jiragen kaya ta tsandauri wata cibiya ce da ke nesa da gabar teku, wadda ake haɗa ta da tashar jiragen ruwa ta teku ta hanyar hanya ko layin dogo.
Ayyukan tashar da a gina a Kebbi
A irin wannan cibiya, ana iya gudanar da ayyukan karɓa da sarrafa kaya, tantancewa da biyan harajin kwastam, adana kaya da sauran hidimomin da suka shafi tashoshin jiragen ruwa.
Ana sa ran tashar da aka tsara ginawa za ta sauƙaƙa wa ’yan kasuwa da masu sana’o’i a Kebbi da jihohin da ke maƙwabtaka da ita wahalhalun jigilar kaya, tare da rage kuɗaɗe da jinkirin da ake fuskanta wajen kai kaya tashoshin jiragen ruwa da ke gabar teku.

Source: Original
Matsayin jihar Kebbi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, da kuma kusancinta da iyakokin ƙasashen waje, ya sa inganta hanyoyin kasuwanci da sufuri ke da muhimmanci ga harkokin kasuwancin jihar.
Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan wurin da za a gina tashar ba, lokacin aiwatar da aikin, yadda za a samar da kuɗin gudanar da shi ko kuma lokacin fara aikin ginin.
Kofa ya hango nasarar Tinubu
Kun ji cewa Hon. Abdulmumin Jibrin ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC za su yi nasara a babban zaben 2027.
Dan Majalisar wakilan a ce dukkan alamu da lissafe-lissafen siyasa na nuna cewa APC da Tinubu za su samu nasara a zaben mai zuwa, inda shugaban kasar ke neman zarcewa karo na biyu.
Asali: Legit.ng
