Barakar cikin kungiyar dattawan Arewa ta kara munana ana saura kwanaki zabe

Barakar cikin kungiyar dattawan Arewa ta kara munana ana saura kwanaki zabe

  • Rikicin shugabanci a ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ya ƙara tsananta duk da taron sulhu da aka shirya
  • Matsalar ta shafi zargin almundahana da kuɗin ƙungiyar, wa'adin shugabanni da wanda ke da ikon tafiyar da harkoki
  • Maganar da ake yi, an rufe sakatariyar ƙungiyar da ke Kaduna, yayin da ɓangarorin da ke takaddama ke zargin juna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Ƙoƙarin a kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana faruwa tsakanin shugabannin ƙungiyar Dattawan yankin Arewa na ACF ya ci tura.

An yi wani taron sirri da ‘yan kwamitin amintattu (BoT), kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da wasu sarakunan gargajiya amma ba a dace ba.

Dattawan Arewa sun zauna a gidan Sarkin Musulmi

Majiyoyin jaridar Daily Trust sun bayyana cewa taron, wanda aka gudanar a ranar Talata a gidan Sarkin Musulmi ya ɗauki tsawon sa'o'i biyu.

Kara karanta wannan

Wike ya fadi abin da zai sa Obi ya gudu a Najeriya ko ya ci zaben 2027

An zauna gidan Mai alfarma Muhammadu Sa'ad Abubakar III, da ke Maitama a Abuja, daga ƙarfe 5:00 zuwa 7:00 na yamma don a daidaita.

Sarakunan da suka halarci taron a Abuja sun haɗa da Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, da Aku Uka na Wukari, Dakta Manu Ishaku Adda Ali.

An ruwaito cewa Sarkin Musulmi Sa'ad III bai halarci taron ba saboda wasu muhimman ayyuka na ƙasa da yake gudanarwa a wani wuri lokacin.

Sarakunan ba su iya sasanta rigimar ACF ba

Majiyoyi sun ce taron ya mayar da hankali ne kan yadda za a kawo ƙarshen rarrabuwar kawuna da ƙungiyar dattawan ke fama da shi tun ba yau ba.

Etsu da Akusun nuna damuwarsu kan yadda kwamitin amintattu da kwamitin zartarwa suka kasa sasantawa.

Shugabannin sun gaza shawo kan matsalolin har su iya zama domin a magance matsalolin tsaro da tattalin arzikin da ke addabar Arewacin Najeriya.

Ɗaya daga cikin sarakunan gargajiyan ya nuna cewa Arewa ta zama abin dariya saboda shugabanninta sun kasa magana da murya ɗaya.

An bayyana cewa taron wani ɓangare ne na jerin ƙoƙarin da ake yi domin sasanta ɓangarorin biyu da ke rigima da juna a kan shugabancin ƙungiyar ACF.

Kara karanta wannan

Shugaban INEC ba ya son a fitar da takardun Tinubu, ya shigar da bukata gaban kotu

Tun farkon shekarar 2026 Sarkin Musulmi da goyon bayan Sarkin Lafia, Sidi Dauda Bage Muhammad da wasu sarakuna suke wannan aiki.

Rigimar kwamitin amintattu da wasu shugabannin ACF

Ana ta fada har shugaban kwamitin amintattun ACF, Bashir Dalhatu, da wasu mambobi sun nemi sakataren ƙungiyar, Malam Murtala Aliyu ya sauka.

Shi Murtala ya ƙi amincewa da hakan, yana mai cewa wa'adinsa zai ƙare ne a Disamban 2026.

An ce wasu mambobin ƙungiyar, ciki har da shugaban kwamitin zartarwa na ƙasa, Mamman Mike Osuman, SAN suna tare da sakataren da aka huro wa wuta.

Baya ga takaddamar shugabanci da wa'adi, batun yadda aka ake riƙe da kuɗi ya haddasa saɓani a AFC.

Rahotanni sun nuna cewa kusan Naira biliyan 3.9 da aka bayar a matsayin gudummawa ga ƙungiyar amma sai aka ajiye su a wani sabon asusu a banki.

An bayar da kuɗin ne a yayin bikin cika shekaru 25 da kafuwar ƙungiyar da aka yi a Nuwamban 2025, sai ba a ajiye su a inda aka saba adana su ba.

Haka kuma, akwai kusan Naira miliyan 700 da wasu shugabannin Arewa suka bayar lokacin bikin, yanzu ana neman jin ya aka yi da maƙudan kuɗin.

Kara karanta wannan

Wike ya tada wa gwamnonin APC 3 hankali da yan takaran da ya kawo jihohinsu

An rufe sakatariyar ƙungiyar ACF a Kaduna

A ranar Litinin ne 'yan sanda suka rufe sakatariyar ƙungiyar ACF a Kaduna. A halin yanzu ana ta zargin juna dangane da abin da ya faru.

Wata majiya daga ɓangaren Bashir Dalhatu ta zargi kwamitin zartarwa ƙarƙashin Mike Osuman da fara rufe sakatariyar domin hana a yi taro.

A wani gefe kuma, su Osuman sun zargi mutanen da ke tare da Bashir Dalhatu da kutsa kai cikin ofisoshin ƙungiyar kuma suka sauya makullai.

Abin bai tsaya nan ba, an ji cewa an kuma umarci ma'aikatan ƙungiyar da su dakatar da zuwa aiki har na tsawon mako guda sakamakon rikicin.

Hakan ya biyo bayan gayyatar wasu ma'aikatan ACF guda uku da 'yan sanda suka yi a ranar 5 ga Nuwamba, ciki har da ma'ajin kuɗin ƙungiyar.

An tafi da su Abuja domin yi musu tambayoyi, inda daga bisani aka sake su bayan sun rubuta bayanansu.

Bukar Zarma, wani daga ɓangaren Dalhatu, ya tabbatar da cewa an sauya makullan sakatariyar, amma ya bayyana dalilin win wannan aiki.

Kara karanta wannan

Abu ya gagara karewa: Gwamna Radda ya fadi yadda zai dakile matsalar tsaro

Zarma ya ce an yi haka ne saboda 'yan kwamitin amintattu su samu damar shiga ofishin ya yi taro. Ita ma jaridar Leadership ta kawo labarin rikicin.

Shi kuma Murtala Aliyu da ake rikici da shi, ya ce sun umarci ma'aikatan ACF da su zauna a gida ne saboda ganin irin cin zarafin da suke fuskanta.

Sa-in-sar manyan Arewa ta kai wajen Gwamnan Kaduna

Shugaban kwamitin zartarwa na ƙasa, Mamman Mike Osuman, ya kai ƙara ga Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, kan abin da yake faruwa.

A cikin ƙarar da ya rubuta ranar 9 ga Nuwamban 2026, ya zargi Munir Mustapha da Bukar Zarma da shiga hedikwatar ƙungiyar da ƙarfi da yaji.

Ya sanar da gwamnan da kuma jami’an tsaro cewa an sauya makullan ofisoshi kuma aka kwashe kayayyaki ba tare da izinin shugabanni ba.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta zargin cewa tana da hannu wajen rufe sakatariyar ACF.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ahmed Maiyaki ya tuna wa jama’a cewa ACF ƙungiya ce da aka kafa domin haɗa kan al'ummar yankin Arewa.

Kwamishinan ya ce Gwamna Uba Sani yana goyon bayan zaman lafiya, haɗin kai da zaman tare, ya kuma ce ba su yi wa 'yan ACF katsalandan ba.

Kara karanta wannan

Zaɓi 2 da suka rage wa Atiku bayan rushe takararsa, shugabannin ADC

Sheikh Dangungu ya tono Ƙungiyar Izala

Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis Sunnah za su gwabza da Usman Dangugu a kotu idan bai nemi afuwar zarginta da kashe Yahaya Masssuka ba.

Ƙungiyar JIBWIS ta hannun lauyoyinta ta ba malamin da yake tafarkin Kur'ani zallah wa'adin kwanaki bakwai ya lashe amansa kuma ya nemi afuwarta.

An samu labari cewa Izala tana zargin Usman Dangugu ya yi magana ne ba tare da wata hujja ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng