INEC Ta Juyo kan Matasan Najeriya, Ta Yi Masu Gargadi kan Zaben 2027

INEC Ta Juyo kan Matasan Najeriya, Ta Yi Masu Gargadi kan Zaben 2027

  • INEC ta yi kira ga matasan Najeriya da su ƙi shiga rikicin siyasa, tsoratar da masu zaɓe da lalata kayan zaɓe
  • Hukumar ta gargaɗi matasa kan laifuffukan zaɓe da suka haɗa da sayen ƙuri’u, satar akwatunan zaɓe da tunzura jama’a
  • INEC ta bukaci matasa su riƙa tantance sahihancin bayanai kafin yaɗa su a kafafen sada zumunta, tare da dogaro da majiyoyin hukuma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bukaci matasan Najeriya da su ƙi shiga tashin hankalin zaɓe, amfani da siyasa wajen yaudarar jama’a, yaɗa ƙiyayya da kuma bayanan ƙarya gabanin babban zaɓen 2027.

Hukumar ta yi wannan kira ne ranar Talata, 17 ga Nuwamban 2026, yayin wani taron tattaunawa da ƙungiyoyin matasa da aka zaɓa a Legas.

INEC ta ja kunnen matasa kan zaben 2027
Shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Joash Amupitan Hoto: Legit.ng
Source: Facebook

Sashen kula da jinsi da haɗa kan al’umma na INEC ne ya shirya taron domin ƙarfafa rawar matasa a harkokin zaɓe da dimokuraɗiyya, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Majalisar Dattawa na son INEC ta hana wasu 'yan takara tsayawa zaben 2027

INEC ta gargaɗi matasa kan tashin hankali

Kwamishiniyar zaɓe ta jihar Legas (REC), Farfesa Ayobami Salami, wadda sakatariyar gudanarwa, Olori Tadese Adenike, ta wakilta, ta ce matasa na da muhimmiyar rawa wajen bunƙasa dimokuraɗiyyar Najeriya.

Ta bayyana cewa halayen matasa kafin zaɓe, lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓe za su taimaka wajen tantance sahihancin sakamakon zaɓukan.

A jawabin maraba da ta gabatar, Olori Tadese ta bukaci matasa su ƙi amincewa da duk wani ɗan siyasa da zai ɗauke su aiki domin tayar da hankali, tsoratar da masu zaɓe ko lalata kayan zaɓe.

“Babu wata buƙata ta siyasa da ta kai darajar rayuwar ɗan Najeriya. Haka kuma, babu nasarar zaɓe da za ta halatta lalata al’umma ko makomar matasa.” In ji ta.

Ta bayyana cewa manufar taron ita ce bai wa matasa bayanan da za su taimaka musu su zama jakadun zaman lafiya, tare da zama abokan hulɗa masu muhimmanci a harkokin zaɓe.

Kara karanta wannan

Masu shirin magudi a zaben 2027 na ruwa, an kai lamarin gaban Shugaba Trump

An shawarci matasa su mutunta ra’ayoyin siyasa

Olori Tadese ta kuma bukaci mahalarta taron su mayar da hankali kan muhimman batutuwan da suka shafi al’umma, maimakon rikici da bambancin ra’ayin siyasa.

Ta ce ya kamata matasa su mutunta ra’ayoyin waɗanda ba sa goyon bayan jam’iyyarsu, tare da amincewa da sakamakon zaɓe ta hanyoyin da doka ta tanada.

Ta ja hankalinsu kan Dokar Zaɓe ta 2026, inda ta bayyana cewa laifuffukan da suka haɗa da sayen ƙuri’u, satar akwatin zaɓe, tsoratar da masu zaɓe da yin kwaikwayon wani mutum na iya jawo hukunci a gaban doka.

Sauran laifukan sun haɗa da hana jami’an zaɓe gudanar da aikinsu da kuma tunzura jama’a su aikata tashin hankali.

INEC ta gargadi matasa kan bayanan ƙarya

Dangane da amfani da kafafen sada zumunta, jami’ar ta shawarci matasa su tabbatar da sahihancin duk wani bayani kafin su yaɗa shi.

Ta kuma bukace su da su riƙa dogaro da sahihan majiyoyin hukuma domin guje wa yaɗa labaran ƙarya da ka iya haddasa rikici.

Kara karanta wannan

An hango abin da zai faru idan aka yi wa 'yan Najeriya karfa karfa kan Tinubu a 2027

INEC ta gargadi matasan Najeriya
Farfesa Joash Amupitan na jawabi a wajen taro Hoto: @inecnigeria
Source: Facebook

Kotu ta soke takarar sanatan APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na APC na kujerar Sanatan Benue ta Arewa maso Gabas.

Mai shari’a Inyang Ekwo ne ya yanke hukuncin a shari’ar da aka yi wa alama da lamba FHC/ABJ/CS/1470/2026, wadda Gabriel Suswam ya shigar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng