Abin da Ya Rage a Ƙaddamar da Ƴan Sandan Jihohi a Najeriya duk da Ƙorafin Ƴan Adawa

Abin da Ya Rage a Ƙaddamar da Ƴan Sandan Jihohi a Najeriya duk da Ƙorafin Ƴan Adawa

  • Majalisar Dattawa ta kammala dukkan matakan gyaran kundin tsarin mulki domin kafa rundunar ’yan sandan jihohi
  • Majalisar ta yanke shawarar aika kudirin dokar ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sanya wa hannu tare da tabbatar da amincewarsa
  • Sanatoci sun kuma bukaci Tinubu ya aika da kudirin dokar rundunar ’yan sanda ta ƙasa domin samar da tsarin gudanar da aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Majalisar Dattawan Najeriya ta sanar da kammala dukkan matakan gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar domin kafa rundunar ’yan sandan jihohi, bayan majalisun dokokin jihohi 36 sun amince da kudirin dokar.

Majalisar ta kuma yanke shawarar aika kudirin dokar ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sanya wa hannu.

Saura kiris a kaddamar da yan sandan jihohi
Sufeta-janar na yan sanda, Rilwan Disu da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga, Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Wannan mataki ya biyo bayan wani kudirin gaggawa da shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele, ya gabatar a zaman majalisar ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba, 2026, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Muhimmin tarihi da Tinubu ya kafa game da yaki da ta'addanci a Najeriya

Bamidele ya bayyana cewa kudirin dokar ya cika dukkan sharuddan da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanada domin yin gyara.

Majalisa ta bayyana yadda aka kammala matakan

Kudirin dokar mai suna Constitution of the Federal Republic of Nigeria (Sixth Alteration) Bill, 2026, na neman kafa rundunar ’yan sandan jihohi a matsayin wani bangare na tsarin aikin ’yan sanda a Najeriya.

Sanata Bamidele ya tuna cewa Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai sun amince da kudirin dokar a ranakun 24 ga watan Yuni da 23 ga watan Yuli, 2026.

Ya ce majalisun biyu sun amince da kudirin ne da rinjayen kuri’un da suka haura kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisar, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Daga bisani, an aika kudirin ga majalisun dokokin jihohi 36 domin su bayyana matsayarsu kan gyaran dokar bisa sashe na 9(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Sanatan mai wakiltar Ekiti ta Tsakiya ya tabbatar da cewa dukkan jihohin 36 sun aika da sakamakon amincewarsu ga Majalisar Tarayya.

Kara karanta wannan

An zabi sabon shugaban majalisar Isra'ila, Netanyahu ya rasa karfin iko

Saboda haka, ya bukaci majalisar ta ba magatakardar Majalisar Tarayya izinin aika kudirin ga Shugaba Tinubu domin sanya hannu, bisa tanadin dokar tabbatar da sahihancin dokoki ta shekarar 2004.

An kusa kammala dokar ya sandan jihohi
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin zaman majalisar zartarwa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Majalisa ta yaba wa Bola Tinubu

Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Bamidele, lamarin da ya kawo karshen matakan majalisa kan kudirin dokar, tare da bude hanyar da Shugaba Tinubu zai duba ta.

Sanatocin sun kuma yabawa shugaban ƙasar bisa goyon bayan da ya bayar wajen ganin an cimma nasarar wannan kudiri.

A cikin kudirin nasu, sun ce:

“Muna godiya ga Mai Girma Shugaban Ƙasa bisa yadda ya dauki wannan kudiri a matsayin nasa tare da nuna jarumtar goyon bayansa a duk tsawon wannan tsari.”

Sai dai majalisar ta bayyana cewa kammala gyaran kundin tsarin mulki kadai ba zai wadatar wajen fara aiki da rundunar ’yan sandan jihohi ba.

Saboda haka, ta bukaci Tinubu ya aika da kudirin dokar rundunar ’yan sanda ta ƙasa zuwa Majalisar Tarayya domin duba shi da kuma amincewa da shi cikin gaggawa.

Abin da ake bukata domin aiwatarwa

Majalisar ta bayyana cewa sabon kudirin dokar zai samar da tsarin gudanarwa da kuma ka'idojin da za a bi wajen fara aiki da rundunar ’yan sandan jihohi.

Kara karanta wannan

An bayyana mutanen da aka kama bayan kai wa Kwankwaso hari a Kano

Ana ganin wannan mataki zai taimaka wajen sauya tsarin aikin ’yan sanda a Najeriya, wanda a halin yanzu yake karkashin ikon gwamnatin tarayya, cewar Vanguard.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kiraye-kirayen samar da rundunar ’yan sandan jihohi domin taimakawa wajen magance matsalolin tsaro da suka addabi sassan ƙasar.

Yan sandan jiha: Matsayar majalisun jihohi

A wani labarin, an ji cewa Majalisun dokokin jihohi 36 na Najeriya sun amince da gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar domin kafa rundunonin ’yan sandan jihohi.

Amincewar ta samu kashi 100 cikin 100, inda ta zarce adadin jihohi 24 da kundin tsarin mulki ya tanada.

Rahotanni sun nuna cewa yanzu an kammala tantance ƙudirin, kuma ana shirin miƙa shi ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sanya hannu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.