Bayan Kalaman Amaechi, An Ji Dalilin da Ya Sa Buhari Bai Zabi Wanda Zai Gaje Shi a APC ba

Bayan Kalaman Amaechi, An Ji Dalilin da Ya Sa Buhari Bai Zabi Wanda Zai Gaje Shi a APC ba

  • Tsohon hadimin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya ce tsohon shugaban ya yi imani da bin tsarin dimokuraɗiyya a cikin jam’iyya
  • Bashir Ahmad ya bayyana cewa Buhari ya janye kansa daga tsoma baki a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa
  • Ya yi fatan waɗanda suka san ƙarin bayani kan alƙawarin da ake zargin Buhari ya yi wa Amaechi za su fito su fayyace lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Tsohon Mataimaki na Musamman kan Kafafen Yaɗa Labarai ga marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya yi martani kan kalaman tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

Bashir ya bayyana dalilin da ya sa Buhari bai fito fili ya goyi bayan burin Rotimi Amaechi na zama ɗan takarar shugaban ƙasa na APC a babban zaɓen 2023 ba.

Kara karanta wannan

Wuta ko aljanna: Trump ya fadi a ina zai iya kasancewa a lahira

Bashir Ahmad.
Tsohon mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad Hoto: Bashir Ahmad
Source: Twitter

Tsohon hadimin Buhari ya yi wannan bayanin ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Bashir Ahmad ya fadi tsarin Buhari

Bashir Ahmad ya ce Buhari ya yi imani da barin tsarin dimokuraɗiyya ya gudana ba tare da katsalandan ba, kuma ba kasafai yake tsoma baki a zaɓen fitar da gwani domin tilasta zaɓen ɗan takarar da yake so ba.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan ikirarin Amaechi cewa Buhari ya yi masa alƙawarin ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa na APC gabanin zaɓen fitarda gwani na jam’iyyar a 2022.

Ya bayyana kalaman Amaechi a matsayin abin mamaki, yana mai cewa hakan bai yi daidai da abin da mutane da dama suka sani game da ƙa’idojin siyasar Buhari da halayensa ba.

'Kalaman Amaechi sun ba da mamaki'

A cewarsa, marigayi shugaban ba ya fitowa ya nuna goyon baya ga wani ɓangare ko dan takara yayin zaɓen fidda gwani na jam’iyya, ko da kuwa yana da ɗan takarar da yake so.

Kara karanta wannan

ADC za ta shiga zaɓen 2027, Keyamo ya ce takarar Atiku ce ke cikin haɗari

Ahmad ya ce:

“Wannan ne dalilin da ya sa kalaman da Rotimi Amaechi ya yi kwanan nan za su ba mutane da dama da suka san Shugaba Buhari, ƙa’idojinsa da halayensa na siyasa mamaki matuƙa.”

Ya bayyana fatan cewa mutanen da suka fi sanin yanayin al’amarin da ya shafi zargin alƙawarin za su fito su yi ƙarin bayani domin kare martabar Buhari.

Amaechi.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi Hoto: Chibuike R. Amaechi
Source: Facebook

Ya kara da cewa:

“Ina fatan waɗanda suka fi sanin wannan al’amari kuma suke da bayanan sirri za su fito su fayyace waɗannan zarge-zarge, tare da taimakawa wajen kare martabar tsohon shugabanmu, wanda dukkanmu muka sani a matsayin mutumin da yake tsayawa kan maganarsa, kuma ba zai taɓa karya alƙawuransa da gangan ba.”

Bashir Ahmad ya kuma tuna da shahararriyar matsayar Buhari kan siyasa, inda ya ce: “Hakika, shi na kowa ne, kuma ba na kowa ba ne.”

Abin da Amaechi ya fada tun farko

Kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi, ya dora alhakin kayen da ya sha a zaben fitar da gwani na APC na 2022 kan Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya bayyana cewa Buhari ya tabbatar masa a rubuce cewa zai ayyana shi a matsayin wanda yake so ya zama dan takarar jam’iyyar a zaben 2023, amma bai yi hakan ha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262