Wuta ko Aljanna: Trump Ya Fadi a ina zai Iya Kasancewa a Lahira

Wuta ko Aljanna: Trump Ya Fadi a ina zai Iya Kasancewa a Lahira

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ba ya son shiga wuta yayin da ya amince cewa matakan korar baƙi da gwamnatinsa ta ɗauka sun yi tsauri
  • Trump ya kuma kare yadda yake tafiyar da tattalin arzikin Amurka da yaƙin Iran, duk da asarar da jam’iyyar Republican ta yi a zaɓen tsakiyar wa’adi
  • Shugaban ya ce ba lallai ya yafewa wasu maƙiyansa na siyasa ba, sannan ya bayyana cewa watakila zai goyi bayan ɗan takarar Republican a 2028

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington, Amurka – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya amince cewa matakan da gwamnatinsa ta ɗauka wajen korar baƙi daga ƙasar sun yi tsauri.

Shugaban ya kuma yi magana kan makomarsa bayan mutuwa, yiwuwar yafewa maƙiyansa na siyasa da kuma wanda zai iya mara wa baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2028.

Kara karanta wannan

Zabe ya wuce, Trump na shirin kaddamar da manyan hare hare Iran

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka na bayani a taro. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da wakilin shirin 60 Minutes, Ross Douthat, kwanaki bayan jam’iyyar Republican ta fuskanci gagarumin kaye a zaɓen tsakiyar wa’adi.

Magana kan korar baki

A yayin hirar, an tambayi Trump kan yadda manufofin shige da fice suka taimaka ko suka cutar da shi a siyasa.

Ya ce matakan rufe iyakokin Amurka sun taimaka masa, inda ya yi ikirarin cewa ya cancanci maki mafi girma saboda hana shigowar baƙi ta haramtacciyar hanya.

Sai dai Trump ya amince cewa an samu matsala wajen korar wasu baƙi da suka shigo ƙasar ba bisa ƙa'ida ba, amma suke da ayyukan yi masu kyau.

Ya ce wasu daga cikin mutanen da aka kora sun kasance masu aiki, kuma laifinsu kawai shi ne shigowa Amurka ba bisa ƙa'ida ba.

Shugaban ya ƙara da cewa matakan korar baƙin sun taimaka masa ta wasu fannoni, amma sun kuma jawo masa matsala a wasu.

Kara karanta wannan

Shugaban Paraguay ya yi murabus saboda gaza shawo kan matsalolin jama'ar shi

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump na duba sama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump bai son shiga wuta

A ƙarshen hirar, Douthat ya tambayi Trump abin da yake tunanin zai faru idan ya mutu, la'akari da cewa ya tsallake yunƙurin kashe shi sau da dama.

Trump ya amsa cewa yana fatan mutane za su riƙa tunawa da shi bayan rasuwarsa.

Da aka tambaye shi ko yana ganin zai shiga Aljanna, shugaban ya ce shi mutum ne mai addini, don haka yana fatan hakan zai kasance.

Sai dai lokacin da aka tambaye shi ko zai iya yafewa maƙiyansa na siyasa domin samun shiga Aljanna, Trump ya ce ba zai iya yin hakan ba.

Da yake magana kan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2028, Trump ya ce akwai yiwuwar ya goyi bayan wani ɗan takarar jam’iyyar Republican, amma hakan ba lallai ba ne.

Ga bidiyon da Trump ya yi bayani a kasa:

Amurka ne neman sirrin Iran

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Amurka ta yi tayin bayar da kyautar dala miliyan 20 ga duk wanda ya ba da sahihan bayanai kan shirin nukiliyar ƙasar Iran.

Kara karanta wannan

"Ko a jiki na," Atiku ya maida martani bayan kotu ta rushe takararsa a zaben 2027

Gwamnatin ta kuma yi alkawarin samar wa masu bayar da bayanan muhimman wurare da kuma yiwuwar sauya musu matsuguni domin kare lafiyarsu.

Wannan tayin ya zo ne duk da ikirarin Shugaba Donald Trump cewa hare-haren da Amurka ta kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran sun lalata su gaba ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng