Dan Takara Ya Ce zai Kifar da Tinubu saboda Dogara ga Allah a 2027
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Seyi Makinde, ya ce yana da yakinin lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 saboda ya dogara ga Allah
- Gwamnan jihar Oyo ya bayyana cewa burinsa na zama shugaban ƙasa ba ya dogara da wani uban gida na siyasa ba ne, sai dai Allah kawai
- Seyi Makinde ya ce yana son gyara Najeriya ta hanyar inganta tsaro, tattalin arziki, ilimi da tsarin zamantakewar siyasar da kasar ke tafiya a kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jos, Filato – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, kuma Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa zai iya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Makinde ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin wani taron ibada a cocin COCIN da ke Jos, jihar Filato, inda ya ce Allah da ’yan Najeriya ne ke mara masa baya.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa daraktan yaɗa manufofinsa, Richard Ihediwa ya ce gwamnan ya ce burinsa na shugabancin Najeriya ya samo asali ne daga bukatar kawo sauyi ta hanyar shugabanci nagari.
Makinde ya dogara ga Allah
Makinde ya bayyana cewa burinsa na zama shugaban ƙasa ba ya samun goyon bayan wani babban ɗan siyasa da zai tsaya masa, sai dai Allah da al’ummar Najeriya.
Ya tuna cewa lokacin da ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan Oyo a shekarar 2018, wasu sun tambaye shi ko yana da wani uban gida a siyasa da zai taimaka masa.
Ya ce ya amsa musu da cewa yana da Allah, kuma daga baya ya samu nasarar zama gwamnan jihar Oyo.
Gwamnan ya ce a wannan karon ma yana da yakinin cewa Allah zai jiƙan Najeriya, ya kuma ba ta shugabancin da ya dace a zaɓen 2027.
Abubuwan da Makinde zai gyara
Ɗan takarar ya bayyana cewa shirinsa na gyara Najeriya zai mayar da hankali kan manyan fannoni huɗu idan har ya yi nasara a 2027.
Vanguard ta rahoto ya ce fannoni sun haɗa da tsaro, tattalin arziki, ilimi da kuma tsarin zamantakewar siyasa.
Makinde ya bayyana cewa gwamnatinsa a jihar Oyo ta dogara ne kan tsare-tsare, gaskiya da riƙon amana, inda aka tsara taswirar ci gaba da ta shafi wa’adinsa biyu daga 2019 zuwa 2027.

Source: Facebook
A yayin gabatar da kundin manufofinsa ga shugabannin cocin COCIN, Makinde ya buƙaci ’yan Najeriya su riƙa yi masa hisabi kan alkawuran da ya ɗauka.
Ya ce ba ya son dogaro da alkawuran baki kawai, saboda ya rubuta dukkan abubuwan da yake son cimmawa a cikin kundin manufofinsa.
Shettima ya caccaki Peter Obi
A wani labarin, mun ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya caccaki Peter Obi bisa zarginsa da yaɗa ƙarya da alkaluma marasa tushe.
Shettima ya bayyana hakan ne a gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da aka gudanar a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
Ya ce Obi ya rasa farin jinin da yake da shi a baya, yana mai cewa yadda yake magana ba ya burge ’yan Najeriya kamar yadda yake a da.
Asali: Legit.ng