Bayan Atiku, Shettima Ya Ce Tamkar Obi ba Ya cikin Takarar 2027 ne a Yanzu
- Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya zargi Peter Obi da lalata damar siyasarsa ta zaɓen 2027 ta hanyar yaɗa ƙarya da alkaluma marasa tushe
- Shettima ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC ya rasa farin jinin da yake da shi a baya kuma kalamansa ba sa burge ’yan Najeriya
- Mataimakin shugaban kasar ya yi waɗannan kalamai ne a wajen gangamin jam’iyyar APC a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, ranar Juma’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Uyo, Akwa Ibom – Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya yi zargin cewa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, ya yi wa kansa illa a takarar zaɓen 2027 saboda yaɗa ƙarya da alkaluma marasa tushe.
Shettima ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom ranar Juma’a.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto ya ce ’yan Najeriya ba sa nuna farin ciki ko sha’awa idan Obi ya yi magana a yanzu, sabanin yadda yake a baya.
Shettima ya caccaki Peter Obi
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce ya samu labarin dawowar Obi Najeriya bayan ya fita ƙasar domin hutawa, inda ya yi iƙirarin cewa tsohon gwamnan na iya kauce wa zuwa Lagos da Abuja bayan dawowarsa.
Shettima ya ce Obi ya lalata damarsa a zaɓen 2027 saboda abin da ya kira ƙarya da amfani da alkaluma marasa tushe.
Ya ƙara da cewa tsohon gwamnan Anambra ya yi asarar farin jinin da ya samu a baya, kuma kalamansa a yanzu na jawo zargi maimakon burge jama’a.
Tinubu ya ƙaddamar da ayyuka
Tun da farko, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da wasu ayyukan raya ƙasa da gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya gudanar.
Daily Trust ta rahoto cewa daga cikin ayyukan akwai sabon ginin tashar jiragen sama ta Victor Attah da ke birnin Uyo.
Tinubu ya bayyana ziyararsa jihar a matsayin komawa gida, inda ya tuna da lokacin da ya yi aiki a kamfanin Mobile da kuma gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa yankin Eket.

Source: Facebook
Tinubu ya yaba wa gwamna Eno
Shugaba Tinubu ya bayyana Gwamna Umo Eno a matsayin jagora mai hangen nesa da kyakkyawar niyyar barin ayyukan ci gaba masu ɗorewa a jihar Akwa Ibom.
Ya ce ƙoƙarin gwamnan wajen bunƙasa jihar ne ya sa gwamnatin tarayya ta amince da sauya matsayin filin jirgin saman Victor Attah zuwa filin da zai riƙa karɓar jiragen ƙasa da ƙasa.
Obi ya goyi bayan Atiku
A wani labarin, kun ji cewa Peter Obi ya nuna damuwa kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta soke zaɓen Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027.
Obi ya ce hukuncin na iya jawo rashin tabbas ga jam’iyyun adawa gabanin zaɓe, tare da shafar damar masu zaɓe wajen zaɓar shugabannin da suke so.
Tsohon gwamnan Anambra ya kuma zargi jam’iyyar mai mulki da amfani da dabarun siyasa wajen raunana jam’iyyun adawa da hana su gudanar da harkokinsu yadda ya kamata.
Asali: Legit.ng

