'Tinubu ba Shi da Karfin Cigaba da Mulkin Najeriya,' APM

'Tinubu ba Shi da Karfin Cigaba da Mulkin Najeriya,' APM

  • Ƙungiyar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta Makinde-Daura (MDPCO) ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye takararsa ta neman wa'adi na biyu a zaɓen 2027
  • Ƙungiyar ta ce Najeriya na buƙatar shugaban ƙasa mai ƙarfi da kuzarin jagorantar ƙasar, tana mai zargin cewa Tinubu ba shi da ƙarfin da ake buƙata domin ci gaba da gudanar da mulki
  • Ta kuma yi kira ga 'yan Najeriya su sabunta katin zaɓensu tare da kaɗa ƙuri'a domin kayar da Tinubu idan bai saurari shawarar da ta ba shi na janye takararsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ƙungiyar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta Makinde-Daura (MDPCO), ƙarƙashin jam'iyyar APM, ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye takararsa ta neman wa'adi na biyu a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

'Ba mu goyon bayan kowace jam'iyya a 2027,' shugaban INEC

Daraktan yaɗa labarai da dabarun sadarwa na ƙungiyar, Richard Ihediwa, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja, yayin da yake mayar da martani kan yawan tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi zuwa ƙasashen waje.

Shugaba Bola Tinubu da Seyi Makinde
Shugaba Bola Tinubu a hagu da Seyi Makinde a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Oyo State Government
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa Ihediwa ya yi magana ne bayan Tinubu ya sake tafiya ƙasar Saudiyya domin gudanar da addu'o'i, makonni kaɗan bayan dawowarsa daga hutun da ya yi a Faransa.

APM ta ce Tinubu ya gaza

Ƙungiyar MDPCO ta bayyana cewa shugaban ƙasar ba shi da ƙarfin jure ƙalubalen gudanar da mulki da kuma yaƙin neman zaɓe, tana mai cewa ya je Makka domin addu'o'i bayan gabatar da jawabi a wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa a Kaduna.

Ihediwa ya ce:

"Shugaba Tinubu ba shi da ƙarfin ci gaba da riƙe muƙamin shugaban ƙasa. Abu ne na dabi'a, dukkanmu muna fatan tsufa, amma bai kamata mu ci gaba da nacewa kan riƙe muƙami ba idan ba mu da ƙwarewa, iko da ƙarfin da za mu gudanar da ayyukan da ke tattare da shi yadda ya kamata.
"Don haka, ya kamata Shugaba Tinubu ya janye ya ba matasa dama su karɓi ragamar mulki. Muƙamin shugaban ƙasa aiki ne mai matuƙar wahala da ke buƙatar ƙarfin jiki."

Kara karanta wannan

Dan Atiku ya kaddamar da gagarumin shiri don tazarcen Tinubu a 2027

Ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da gaza jagorantar ƙasar yadda ya kamata, yana mai cewa Najeriya na ci gaba da koma baya a cikin shekaru uku da rabi da suka gabata.

Gwamna Seyi Makinde
Gwamna Seyi Makinde a wajen taron siyasa. Hoto: Oyo State Government
Source: Facebook

APM ta fifita Seyi Makinde kan Tinubu

Daraktan yaɗa labaran ya bayyana cewa ɗan takararsu na shugaban ƙasa, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, yana da gogewa, shiri da kuzarin da ake buƙata domin jagorantar Najeriya.

Ya ce Makinde zai iya yin aiki dare da rana domin cika alƙawuran da ya ɗauka tare da samar da gwamnatin haɗin kan ƙasa da za ta haɗa kowa da kowa.

Ihediwa ya bayyana cewa:

"Najeriya na buƙatar shugaban ƙasa da zai iya ziyartar dukkan sassan ƙasar, ya shafe lokaci tare da 'yan ƙasa, kuma ya ci gaba da kasancewa cikin harkokin mulki har zuwa tsakiyar dare.
"Wannan ne ya bayyana irin tarbar da 'yan Najeriya suka yi wa Makinde, mataimakinsa Lawal Daura da sauran tawagar yaƙin neman zaɓensu a yankunan Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Gabas, Kudu maso Kudu, Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas."

Ya buƙaci 'yan Najeriya su ci gaba da nuna goyon baya ga jam'iyyar tare da karɓar katin zaɓensu domin kayar da Tinubu a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

2027: Ɗiyar Tinubu ta yi maganar da ka iya tsorata 'yan Najeriya kan Atiku da Peter Obi

Za a sayawa sarakuna motoci

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da sayen sababbin motocin alfarma kirar SUV domin bai wa sarakunan gargajiya a birnin tarayya Abuja.

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyun siyasa da ƙaddamar da 'yan takarar majalisar tarayya a Abuja.

Wike ya ce matakin na shugaban ƙasa ya nuna muhimmancin da yake bai wa sarakunan gargajiya wajen kiyaye al'adu da tabbatar da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng