Gwamna Ya Shirya Kayar da Tinubu a Jihohi 12 a Zaben Shugaban Kasa na 2027
- Ɗan takarar shugaban kasa na APM kuma gwamnan Oyo, Seyi Makinde zai kayar da Tinubu a jihohi 12 da ware a matsayin wadanda zaben 2027 zai yi zafi
- Kwamitin yakin neman zaben shugaban na APM ne ya yi wannan ikirarin yayin da yake maida martani kan matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauka
- Tawagar kamfen Makinde ta ƙara da cewa shawarar Tinubu na zuwa yaƙin neman zaɓe da kansa a jihohi 12 kacal ya nuna fargabarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Makinde-Daura (MDPCO) ya ce APM ta shirya ba shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu mamaki a zaben 2027.
Kwamitin kamfen ya ce ɗan takararta na shugaban ƙasa na APM, Injiniya Seyi Makinde, zai kayar da Tinubu a jihohi 12 da aka bayyana a matsayin wuraren da fafataa za ta yi zafi.

Kara karanta wannan
Shin Tinubu ya karya doka da ya ce ba zai je kamfe wasu jihohin Najeriya ba? An samu bayani

Source: Facebook
MDPCO ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa da Dabarun Yaɗa Labaranta, Hon. Richard Nnanna Ihediwa, ya fitar, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Makinde zai iya kayar da Tinubu
Ya yi ikirarin cewa Gwamna Makinde zai yi galaba a kan Tinubu da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ma jam’iyyar APC a Jihar Rivers da Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.
Kwamitin ya dage cewa babu wani matakin siyasa na makirci, tsoratarwa ko amfani da damar riƙe madafun iko da mutanen Tinubu za su yi da zai iya sauya yadda adawar siyasa ke ƙaruwa da kuma ƙudurin jama’a na hana shi sake komawa kan mulki.
Ya ce girman kai da wuce gona da iri a harkokin siyasa da mutanen da ke kusa da Tinubu ke nunawa sun ƙara jawo fushin jama’a tare da raunana damar sake zaɓen shugaban ƙasar.
APM ta hango fargabar Tinubu
Tawagar kamfen Makinde ta ƙara da cewa shawarar Tinubu na zuwa yaƙin neman zaɓe da kansa a jihohi 12 kacal, Oyo, Kaduna, Rivers, Plateau, Borno, Enugu, Bauchi, Sokoto, Delta, Kano, Adamawa da Lagos, ta ƙara tabbatar da fargabarsa.
Sanarwar ta ce:
“Ya kamata shugaban ƙasa ya sani cewa ziyarar da zai kai waɗannan jihohi, idan har ya je, ba za ta sauya ra’ayin jama’a ko ƙudurin da suka yi na ƙwace mulki daga hannunsa ba.
“Shugaba Tinubu ba shi da wata gagarumar nasara da zai yi alfahari da ita a waɗannan jihohi da sauran sassan ƙasar, inda ’yan Najeriya yanzu ke kiran gwamnatinsa da suna ‘T-Pain’ sakamakon wahalhalun ya jefa su.
MDPCO ta ƙalubalanci Tinubu da kada ya sauya ra’ayinsa, amma ya je jihohin domin ya fuskanci jama’a, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Source: Twitter
Makinde ya ja hankalin yan Najeriya
Kun ji cewa gwamnan Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na APM, Seyi Makinde, ya bukaci ’yan Najeriya su sauke Bola Tinubu daga mulki a zaɓen 2027.
Ya ce ya kamata ’yan Najeriya su yi la’akari da halin da ɓangaren samar da wutar lantarki yake ciki yayin da suke yanke shawarar wanda za su zaɓa a babban zaɓe na gaba.
Asali: Legit.ng
