Tinubu Ya Jingine Bambancin Siyasa, Ya Aika Muhimmin Sako ga Kwankwaso
- Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya taya Kwankwaso murnar cika shekara 70 a ranar 21 ga Oktoba, 2026
- Shugaban ƙasar ya tuna da tarihin alaƙarsu tun shekarar 1992, lokacin da suke Majalisar Dokoki ta Ƙasa
- Tinubu ya ce bambancin jam’iyyunsu da fafatawarsu a zaɓen Janairun 2027 ba zai rage ƙaunar da yake yi wa Kwankwaso ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Shugaba Bola Tinubu ya taya dan takarar mataimakin shugaban kasar na NDC murnar cika shekara 70 da haihuwa a duniya.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne cikin saƙon taya murnar da Tinubu ya fitar a ranar 21 ga Oktoba, 2026, wanda hadiminsa Bayo Onanuga ya sanya a shafinsa na X.
A cikin sakon, Tinubu ya bayyana Kwankwaso a matsayin abokinsa, ɗan siyasa mai tasiri kuma mai ra’ayin kawo ci gaba.
Shugaban ƙasar ya kuma yi wa Kwankwaso fatan samun lafiya, gamsuwa a rayuwa da kuma ƙarin shekaru masu yawa na bayar da gudummawa ga dimokuraɗiyyar Najeriya.
Tinubu ya tuna da tarihin alaƙarsu
Tinubu ya ce alaƙarsa da Kwankwaso ta samo asali ne tun shekarar 1992, lokacin da suke Majalisar Dokoki ta Ƙasa, inda Kwankwaso yake a Majalisar Wakilai, shi kuma Tinubu yake a Majalisar Dattawa.
Ya ce sun sake haɗuwa a fagen shugabancin jihohi a shekarar 1999, lokacin da kowannensu ya zama gwamnan jiharsa.
A cewarsa, kasancewarsu cikin rukunin gwamnonin da suka hau mulki a shekarar 1999 ya ba su damar taka muhimmiyar rawa wajen gina tushen dimokuraɗiyyar da Najeriya ke morewa a yau.
“Ni da Sanata Kwankwaso mun daɗe muna hulɗa, tun lokacin da muke Majalisar Dokoki ta Ƙasa a shekarar 1992, shi a Majalisar Wakilai, ni kuma a Majalisar Dattawa. Daga baya, a shekarar 1999, dukkanmu muka zama gwamnonin jihohinmu."

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya fito ya yi maganar dalilin da ya sa Atiku ba zai iya kifar da Tinubu ba
“A matsayinmu na mambobin rukunin gwamnonin 1999, mun taka muhimmiyar rawa wajen shimfiɗa harsashin dimokuraɗiyyar da ƙasar ke morewa a yau.” In ji shi.
Ya yaba da gudummawar Kwankwaso
Tinubu ya yaba da gudummawar da Kwankwaso ya bayar ga Jihar Kano da Najeriya a matsayinsa na gwamna na wa’adi biyu, tsohon ministan tsaro, tsohon sanata da ɗan takarar shugaban ƙasa.
“Dole ne na amince da gagarumar gudummawar da Sanata Kwankwaso ya bayar ga Jihar Kano da Najeriya a matsayinsa na gwamna na wa’adi biyu, tsohon ministan tsaro, tsohon sanata, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, kuma a yanzu abokin takarar shugaban ƙasa.” In ji shi.
Tinubu ya ƙara da cewa Kwankwaso na ci gaba da kasancewa ɗan siyasa mai tasiri da kuma ra’ayin kawo ci gaba.
Ya ce bambancin jam’iyya ba zai hana abota ba
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa duk da bambancin zaɓin siyasa da suka yi a wasu lokuta, sun sake haɗuwa a shekarar 2013 wajen kafa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Ya ce tun daga lokacin, tarihi da hidimar ƙasa sun ci gaba da haɗa su. Tinubu ya jaddada cewa kasancewarsu a jam’iyyun siyasa daban-daban da kuma fafatawarsu a dandamali daban-daban a zaɓen Janairun 2027 ba zai kawo ƙarshen kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsu ba.
“Kasancewarmu a jam’iyyun siyasa daban-daban da fafatawarmu a dandamali daban-daban a zaɓen Janairun 2027 ba zai kawar da ƙaunar da nake yi wa Sanata Kwankwaso ba.” In ji shi.

Source: Facebook
Sakon Gwamna Abba ga Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tabbaci kan zaben 2027.
Gwamna Abba ya tabbatar wa Shugaba Bola Tinubu cewa Arewa za ta mara masa baya a ƙoƙarinsa na sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

