"Yadda Tinubu Ya Ceci Najeriya daga Fadawa Gagarumar Matsala Irin Ta Kasar Venezuela"

"Yadda Tinubu Ya Ceci Najeriya daga Fadawa Gagarumar Matsala Irin Ta Kasar Venezuela"

  • Jigon APC a Delta, Olorogun O’tega Emerhor ya ce Shugaba Bola Tinubu ya ceci Najeriya daga durkushewar tattalin arziki kamar Venezuela
  • Ya bukaci a yan Najeriya musamman mazauna jihar Delta da su sake zabar Tinubu da Gwamna Sheriff Oborevwori a zaben 2027
  • Emerhor ya ce ya kamata a bai wa Tinubu karin shekaru hudu domin kammala gyare-gyaren tattalin arzikin da ya fara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta, Nigeria - Wani jigon APC a Jihar Delta, Olorogun O’tega Emerhor, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ceci Najeirya daga durkushewa kamar abin da ya faru a Venezuela.

Ya ce ba don jajircewa da hangen nesan Shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiwatar da manyan gyare-gyaren tattalin arziki ba lokacin da ya hau mulki a shekarar 2023, da Najeriya ta fada cikin matsanancin durkushewar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Sanata Dino Melaye ya jagoranci yi wa Tinubu 'Allah Ya isa' ƙafa 3 a gangamin ADC

Olorogun O’tega Emerhor.
Jigon jam'iyyar APC a jihar Delta, Olorogun O’tega Emerhor Hoto: Olorogun O’tega Emerhor
Source: Facebook

Tribune Nigeria ta rahoto cewa Emerhor ya bayyana hakan ranar Alhamis a lokacin kaddamar da yakin neman zaben APC a Jihar Delta, a garin Oleh da ke Karamar Hukumar Isoko ta Kudu.

Emerhor ya yabawa Shugaba Tinubu

Ya dage cewa matakan da shugaban kasar ya dauka, duk da wahalar da suka zo da ita, sun ceci Najeriya daga bakin durkushewar tattalin arziki.

Jigon APC din ya kuma yi kira da a sake zabar Shugaba Tinubu da Gwamnan Jihar Delta, Rt. Hon. Sheriff Oborevwori, a zaben 2027.

Ya ce shugabannin biyu sun nuna kwarewar da ake bukata wajen sake fasalin tattalin arzikin kasa da jihar, tare da bunkasa ababen more rayuwa domin samun ci gaba mai dorewa.

Ta ya Bola Tinubu ya ceci Najeriya?

A cewar Emerhor, Najeriya na dab da fuskantar matsalar tattalin arziki mai kama da wadda Venezuela, kasa mai arzikin man fetur da ke Kudancin Amurka, ta shiga.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya bar ƙasar Saudiyya bayan kammala Umrah, an ji birnin da zai sauka

Ya ce:

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ceci Najeriya. Da shugaban kasarmu bai dauki wadannan matakai masu karfin hali ba, da Najeriya ta bi sahun Venezuela. Shin kuna son Najeriya ta zama wata Venezuela?
“Venezuela ta fi Najeriya yawan man fetur, amma rashin shugabanci nagari da shekaru na rashin kyakkyawan tafiyar da tattalin arziki sun lalata tattalin arzikinta. Tsawon shekaru da dama, irin wannan shugabanci ne muka fuskanta a Najeriya.”

Jigon APC ya soki ’yan adawa

Emerhor ya soki wasu ’yan siyasar adawa da ke shirin kalubalantar Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ya yi zargin cewa da dama daga cikinsu sun kasance cikin tsarin siyasar da ke da alhakin matsalolin tattalin arzikin da kasar ta dade tana fuskanta.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wani taro na kasa da kasa da ya halarta Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ya dage cewa jajircewar Tinubu da kudurinsa na siyasa ne suka sa aka fuskanci manyan matsalolin tsarin tattalin arzikin da gwamnatocin baya suka kasa magancewa.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya kuma magana, ya ba Tinubu shawarar da za ta taimaki gwamnatinsa

Gwamnan Delta ya goyi bayan Tinubu

Kun ji cewa Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, ya bayyana goyon bayansa dari bisa dari ga shugaba Bola Tinubu a babban zaben 2027 da ke tafe.

Oborevwori ya bayyana cewa zai zama abin da bai dace ba ga mazauna jihar Delta su kada kuri’ar kin goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓenshugaban ƙasa na 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262