Shugaba Tinubu Ya Bar Kasar Saudiyya bayan Kammala Umrah, An Ji Birnin da Zai Sauka

Shugaba Tinubu Ya Bar Kasar Saudiyya bayan Kammala Umrah, An Ji Birnin da Zai Sauka

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bar birnin Jeddah domin dawowa gids Najeriryan bayan kammala aikin Umrah a birnin Makkah
  • Bola Tinubu ya yi addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya, tsaro, haɗin kai da wadata a Najeriya
  • Tinubu ya gode wa Sarkin Saudiyya da Yarima mai jiran gado bisa karimci da damar shiga cikin Ka’aba domin yin sallah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taso daga filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah, ƙasar Saudiyya, zuwa Abuja a ranar Laraba, bayan kammala aikin Umrah.

Tinubu ya kamo hanyar dawowa gida Najeriya ne bayan kammala ziyarar da ya kai kasar Saudiyya, inda ya yi ibadu da addu'o'i ga kowane dan Najeriya.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da tawagarsa da wasu jami'an Saudiyya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tinubu ya baro Saudiyya zuwa Abuja

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook yau Laraba, 4 ga watan Nuwamba, 2026.

Kara karanta wannan

An fara batun Tinubu ya je Umrah ne don neman kuri'un 'yan Arewa, hadiminsa ya magantu

Sanarwar ta ce jirgin shugaban ƙasar ya tashi daga sashen jiragen sarauta na filin jirgin saman Sarki Abdulaziz da misalin ƙarfe 5:13 na yamma agogon Saudiyya.

Mataimakin Gwamnan Makkah, Yarima Saud bin Mishaal bin Abdulaziz Al Saud, Jakadan Najeriya a Saudiyya, Ambasada Yakubu Gambo, da Babban Jami’in Ofishin Jakadanci, Ambasada Muazam Ibrahim Nayaya, ne suka raka Tinubu.

Kafin tafiyarsa, Shugaba Tinubu ya yi ɗan gajeren ganawa da mataimakin gwamnan yankin Makkah a fadar baƙi ta sarauta da ke filin jirgin saman.

Ayyukan da Tinubu ya yi a Makkah

A ranar Alhamis, bayan isarsa Saudiyya, shugaban ƙasar ya jagoranci tawagar Najeriya wajen gudanar da ibadar Umrah, ciki har da dawafi a kusa da Ka’aba mai tsarki.

A ranar Lahadin da ta gabata, an ba Shugaba Tinubu damar shiga cikin Ka’aba, wata dama da ba kasafai ake samu ba. A can ne shi da mambobin tawagarsa suka gudanar da sallahnraka’a biyu.

Kara karanta wannan

Maganar da Abdussamad Rabiu ya yi bayan bude masu ka’aba tare da Tinubu

A cikin Ka’aba mai tsarki, shugaban ƙasar ya yi addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya mai ɗorewa, tsaro, haɗin kai da wadata a Najeriya.

Ya kuma roƙi Allah ya ba shi shiriya, hikima da ƙarfi domin ci gaba da yi wa al’ummar Najeriya hidima.

Tinubu ya yi wa Najeriya addu'o'i

Shugaba Tinubu ya kuma roƙi Allah Ya ci gaba da yi wa Najeriya, shugabanninta da al’ummarta albarka. Ya bayyana fatan cewa bambancin da ke tsakanin al’ummar ƙasar zai zama tushen ƙarfi, haɗin kan ƙasa da wadata da kowa zai amfana da ita.

Ziyarar shugaban ƙasar zuwa Saudiyya ta ba shi damar yin nazari kan addini, godiya ga Allah da kuma addu’o’i domin Najeriya.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana sauko sa daga jirgi bayan dawowa daga wata tafiya Hoto: @onanuga1956
Source: Twitter

Haka kuma, ziyarar ta ƙarfafa aniyarsa ta ci gaba da aikin gina ƙasa mai zaman lafiya, haɗin kai da wadata.

"Shugaba Tinubu ya baro Saudiyya da ƙarin ƙarfin imani, godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da kuma ƙudurin ci gaba da aiwatar da shirin Renewed Hope Agenda, tare da burin gina Najeriya mafi kyau ga kowa," in ji Onanuga.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi wa kowane ɗan Najeriya addu'a a ziyarar da ya kai ƙasar Saudiyya

Tinubu ya kammala ziyara a Saudiyya

Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da kammala ziyarar da ya kai kasar Saudiyya domin yin ibada da addu'o'i ga Najeriya.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce ya yi addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da wadata ga Najeriya da al’ummarta a yayin ziyarar da ya kai Masarautar Saudiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262