Aiki Ya Samu Kwamishinoni a Jihohi, Gwamnatin Tinubu Ta ba Su Abin Yi kan Zaɓe
- Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya buƙaci kwamishinonin yaɗa labarai na APC su haɗa kai wajen isar da manufofi da nasarorin Bola Tinubu
- Idris ya ce ya kamata gwamnatocin jihohi da na tarayya su ƙarfafa haɗin gwiwa wajen yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya da rashin sahihanci
- Kwamishinonin yaɗa labarai 20 daga jihohin da APC ke mulki sun halarci taron da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
ABUJA – Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa, Mohammed Idris, ya buƙaci kwamishinonin yaɗa labarai na jam’iyyar APC a jihohi su ƙarfafa haɗin gwiwa.
Ministan ya ce wajibi ne su haɗa kai wajen isar da manufofi da nasarorin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga ’yan Najeriya.

Source: Facebook
Idris ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya gudanar da kwamishinonin yaɗa labarai na APC a Abuja wanda muka gano an wallafa a shafin ma'aikatar.

Kara karanta wannan
Gwamna ya yi magana mai zafi kan harin da aka kai wa ayarin Peter Obi da Kwankwaso
Idris ya fadi muhimmancin yaɗa manufofin Tinubu
Ministan ya bayyana cewa ingantaccen yaɗa labarai muhimmin ginshiƙi ne wajen gudanar da shugabanci nagari da tabbatar da fahimtar manufofin gwamnati.
Ya ce wajibi ne a tabbatar ’yan Najeriya sun fahimci manufofin shirin Renewed Hope, ƙalubalen da ke tattare da shi da kuma amfanin da ake sa ran samu.
A cewarsa, sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa na da nufin ƙarfafa tattalin arziki, samar da damammaki, inganta ababen more rayuwa da bunƙasa ƙasa.
Idris ya jaddada cewa yaɗa sahihan bayanai ba wani zaɓi ba ne, illa wani muhimmin ɓangare na shugabanci da hulɗa tsakanin gwamnati da al'umma.

Source: Twitter
Ya yi gargaɗi kan yaɗa bayanan ƙarya
Ministan ya buƙaci kwamishinonin su ƙarfafa hanyoyin sadarwa tsakanin hukumomin gwamnatin tarayya da na jihohi domin tabbatar da sahihancin bayanan da ake fitarwa.
Ya kuma bukaci su yi amfani da kafafen yaɗa labarai na gargajiya da na zamani wajen isar da saƙonnin gwamnati ga jama'a.

Kara karanta wannan
"Nan ba da daɗewa ba yan Najeriya za su fara murna da tsare tsaren Shugaba Tinubu"
Haka kuma, ya gargaɗi kwamishinonin kan yaɗa bayanan ƙarya da waɗanda aka karkatar da su, yana mai cewa gaskiya da riƙon amana suna da muhimmanci.
Ya bayyana cewa amincewar al'umma ita ce babbar kadarar gwamnati, kuma sahihanci, gaskiya da daidaito wajen sadarwa ne za su taimaka wajen kiyaye wannan amincewa.
Idris ya bukaci gwamnati ta saurari ra'ayin jama'a
Ministan ya kuma jaddada muhimmancin sauraron koke-koken jama'a da fahimtar ra'ayoyinsu wajen tsara dabarun yaɗa bayanan gwamnati.
Ya ce sadarwa ba abu ne da gwamnati ke yi ita kaɗai ba, domin ya kamata a riƙa sauraron jama'a tare da la'akari da shawarwarinsu.
A cewarsa, taron ya samar da dama wajen gina dangantaka mai ɗorewa tsakanin masu kula da yaɗa labarai a matakan gwamnati daban-daban.
Kwamishinonin yaɗa labarai 20 daga jihohin da APC ke mulki ne suka halarci taron, inda suka tattauna hanyoyin ƙarfafa sadarwa tsakanin gwamnatoci da inganta hulɗa da jama'a.
Minista ya yi magana kan rusa takarar Atiku
An ji cewa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya yi maraba da hukuncin kotu da ya rusa shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark.
Keyamo ya ce ƙungiyar haɗakar da ta karɓi ragamar jam’iyyar ba ta samu izinin hukumomin ADC ba kafin ta gudanar da sauye-sauyen shugabanci.
A nasa martanin, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da kotu da wasu dabaru domin kawo cikasa.
Asali: Legit.ng
