Gwamnatin Tarayya Ta Ware Gwamna 1 a Arewa, Ta Yaba Masa kan Ayyukan Alheri
- Ministan Yaɗa Labarai a Najeriya Mohammed Idris, ya yi ruwan yabo ga Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago kan ayyukan alheri
- Gwamnatin tarayya na shirin kashe kusan Naira tiriliyan 1.5 wajen faɗaɗa da sake gina babbar hanyar Lambata zuwa Kontagora
- An shirya aza harsashin aikin hanyar a Bida ranar 13 ga Oktoba, domin sauƙaƙa jigilar amfanin gona da bunƙasa harkokin kasuwanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa, Mohammed Idris, ya yaba wa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago.
Idris ya yaba masa ne kan zuba jarin gwamnatinsa a fannin noma, ababen more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki, tare da jaddada muhimmancin aikin babbar hanyar tarayya da za a kashe kusan Naira tiriliyan 1.5 a jihar.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa ma'akatar ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma’a, 9 ga Oktobar shekarar 2026.
Hadin guiwar Neja da gwamnatin tarayya
Idris ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci mambobin Ƙungiyar Ci Gaban Jihar Neja (NSDF) zuwa ziyarar girmamawa ga Bago a Abuja.
Ministan ya yaba da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da gwamnatin Neja, yana mai bayyana jihar a matsayin muhimmiyar jiha ga ci gaban Najeriya saboda damar noma da take da ita, matsayinta na ƙasa da kuma gudummawar da take bayarwa ga samar da wutar lantarki ta ƙasa ta tashoshin samar da wutar lantarki na Kainji, Jebba da Shiroro.
Idris ya ce:
“Zuba jarin da gwamnatinku ke yi a fannin noma, ababen more rayuwa, sabunta birane da bunƙasa tattalin arziki yana shimfiɗa muhimman tubalan sauyi da ci gaban jiharmu.”
Ya yaba wa Bago kan mayar da hankali ga aikin gona na zamani da injuna, noma na kasuwanci da bunƙasa masana’antun sarrafa amfanin gona, yana mai cewa waɗannan fannoni na da muhimmanci ga bunƙasar tattalin arzikin jihar.

Source: Twitter
Minista ya yaba wa kokarin Tinubu a Neja
Ministan ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan aikin sake gina babbar hanyar tarayya ta Lambata–Bida–Mokwa–Makera–Kontagora tare da faɗaɗa ta zuwa hanyoyi biyu masu tafiya a saɓani, wanda za a kashe kusan Naira tiriliyan 1.5. An tsara aza harsashin fara aikin a Bida ranar 13 ga Oktoba, 2026.
Idris ya ce:
“Wannan gagarumin aiki ne a ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin noma da kasuwanci a Najeriya.
Hanyar za ta inganta isa ga al’ummomin manoma, haɗa kasuwanni da cibiyoyin masana’antu, tare da sauƙaƙa jigilar amfanin gona, kayayyaki da mutane.”
Ministan ya ce aikin zai taimaka wajen bunƙasa harkokin tattalin arziki ta hanyar inganta hanyoyin haɗa al’ummomin manoma da kasuwanni da cibiyoyin masana’antu da ke kan wannan hanyar.
Minista ya yaba wa salon mulkin Tinubu
An ji cewa Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya kwararo yabo ga gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Alhaji Mohammed Idris ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta yi wa waɗanda suka gabace ta nisa nesa ba kusa ba.
Ministan ya nuna cewa gwamnatin ta samu nasarori waɗanda gwamnatocin baya ba su same su ba a cikin shekara biyu.
Asali: Legit.ng


