Sabon Umarnin da APC Ta ba Ministoci da Masu Mukamai kan Kamfen din Tinubu
- Shugaban Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC, Abdulaziz Yari, ya bayar da umarni ga ministoci da masu muƙaman siyasa
- Kwamitin ya buƙaci jami’an siyasa su mayar da hankali kan wayar da kan magoya baya a rumfunan zaɓe, unguwanni da ƙananan hukumominsu
- APC ta ce za ta yi amfani da gangamin wajen tallata ’yan takararta na kujerun majalisun dokokin jihohi, wakilai da dattawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC (PCC) ya umarci ministoci, masu riƙe da muƙaman siyasa da mambobin kwamitin da su halarci gangamin yaƙin neman zaɓen 2027 da aka shirya gudanarwa a jihohinsu na asali kawai.
An bayyana umarnin ne a cikin wata takardar sanarwa da darakta-janar na kwamitin, Abdulaziz Yari, ya sanya wa hannu.

Source: Twitter
A cewar takardar, manufar gangamin ita ce tattara magoya bayan APC da kuma sanar da masu zaɓe irin nasarorin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu tun bayan hawansa mulki, TheCable ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan
El Rufai ya aiko sako ga masoya da magoya baya kan 'yan takarar da za su zaba a 2027
Umarnin da aka bai wa ministoci
Kwamitin ya buƙaci ministoci da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa da su mayar da hankali kan wayar da kan jama’a a matakin tushe.
Ya ce ya kamata su gudanar da wannan aiki a rumfunan zaɓensu, mazabunsu da ƙananan hukumominsu, bisa tsarin da ya kira “Pyramid Concept”.
Takardar ta ce:
“Ana buƙatar ministoci da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa su halarci gangamin da aka shirya gudanarwa a jihohinsu na asali kawai. Wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da ingantaccen tsari da gudanar da ayyukan yaƙin neman zaɓe.”
Haka kuma, kwamitin ya umarci sassan da ba su da takamaiman nauyin gudanar da wani aiki a gangamin da su mayar da hankali wajen aiwatar da tsare-tsarensu da kasafin kuɗin da aka amince musu.
Abin da aka umarci shugabannin APC na ƙasa
Yari ya kuma yi bayani kan rawar da mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na APC za su taka yayin gudanar da gangamin.

Kara karanta wannan
An fara batun Tinubu ya je Umrah ne don neman kuri'un 'yan Arewa, hadiminsa ya magantu
Ya ce mambobin kwamitin, ban da shugaban jam’iyya na ƙasa, sakataren jam’iyya na ƙasa, shugabar mata ta ƙasa, shugaban matasa na ƙasa da sakataren tsare-tsare na ƙasa, ya kamata su fi mayar da hankali kan ayyukan jam’iyya da tattara magoya baya a jihohinsu da yankunansu.
Sai dai takardar ta bayyana cewa dukkan mambobin NWC ana sa ran za su halarci gangamin da aka shirya gudanarwa a jihohinsu na asali.
APC za ta tallata ’yan takararta a gangamin
Kwamitin ya ce zai yi amfani da gangamin wajen ƙara fito da ’yan takarar APC da ke neman kujerun majalisun dokokin jihohi, Majalisar Wakilai ta Tarayya da Majalisar Dattawa.
Wannan na nufin gangamin ba zai tsaya kan tallata takarar Shugaba Tinubu kaɗai ba, domin zai kuma ba sauran ’yan takarar jam’iyyar damar bayyana manufofinsu ga masu zaɓe.
A ƙarshen takardar, Yari ya buƙaci daraktocin sassan kwamitin da su tabbatar da cewa dukkan jami’an da ke ƙarƙashinsu sun samu sanarwar umarnin, tare da bin dukkan ƙa’idojin da aka shimfiɗa.

Source: Facebook
Sanusi II ya gargadi gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi gargadin cewa yawan bashin da Najeriya ke karba da almubazzarancin kudaden gwamnati na barazana ga dorewar tattalin arzikin kasar.
Sanusi II ya bukaci gwamnatin tarayya ta rungumi tsarin kula da kashe kudade, tare da mayar da hankali kan muhimman bangarorin da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki.
Asali: Legit.ng